Gagarumar gobara ta lashe shaguna a kasuwar kayan gyaran motoci ta Kaduna

Gagarumar gobara ta lashe shaguna a kasuwar kayan gyaran motoci ta Kaduna

- Shaguna a kasuwar safayar kayan motoci da ke yankin Oriapata da ke Kaduna sun babbake

- An gano cewa mummunan gobarar ta tashi ne a cikin daren Juma'a bayan kamawar shago 1

- Shugabannin kungiyar 'yan kasuwar sun roki gwamnatin jihar Kaduna da ta kawo musu dauki

Shaguna masu tarin yawa da ke kasuwar siyar da safayan kayan motoci da ke titin Jos a yankin Oriapata da ke jihar Kaduna sun babbake sakamakon gobarar da ta tashi.

Duk da har yanzu ba a gano musababin wutar ba da ta tashi a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 'yan kasuwa da mazauna yankin sun tabbatarwa da Channels TV cewa gobarar ta fara ne bayan da wani shago daya ya fara babbaka.

Shugabannin kungiyar 'yan kasuwan masu siyar da bangarorin motocin sun ce gobarar ta yi mummunar barna tunda ta shafi kayan kudi masu tarin yawa.

KU KARANTA: COVID-19: Daga bisani, El-Rufai ya amince a bude dukkan makarantu

Gagarumar gobara ta lashe shaguna a kasuwar kayan gyaran motoci ta Kaduna
Gagarumar gobara ta lashe shaguna a kasuwar kayan gyaran motoci ta Kaduna. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

Shugaban kungiyar 'yan kasuwa masu siyar da safayar motocin reshen jihar Kaduna, Cyprian Eneje ya yi kira ga gwamnatin jihar kaduuna da ta kawo musu dauki domin ba su damar fara sabon kasuwanci.

A halin yanzu, jihar Kaduna da wasu sassan arewa suna fuskantar matsanancin sanyin gari wanda ya dawo bayan kwanakin kadan da yin saukinsa.

A wannan lokacin ne kuwa ake ta fama da muguwar gobara wacce take lashe kasuwanni ko kuma gidaje.

KU KARANTA: Da duminsa: Saraki da jiga-jigan PDP sun yi ganawar sirri da IBB, Abdulsalami

A wani labari na daban, gwamna Nasir El-Rufai ya baiwa matasa shawarwari da dabarun da za su fatattaki tsofaffi irinsa daga siyasa.

A wata tattaunawa da 'Radio Now's Urgent Conversation' dake jihar Legas suka yi dashi a ranar Juma'a, ya yi kira ga matasa, kwararru a fannoni daban-daban da kuma shugabannin addini da su hada kawunansu wurin ciyar da siyasa da kasar nan gaba.

El-Rufai ya ce zanga-zanga da tayar da hankula ba za su kai kowa ko ina ba har sai mutanen kirki sun taru sun mika kawunansu ga taimakon kasarsu ta gado, Daily Trust ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel