Kwankwaso ya bada gudunmuwan kayan abinci ga Hausawan da rikicin Shasha a Oyo ya shafa

Kwankwaso ya bada gudunmuwan kayan abinci ga Hausawan da rikicin Shasha a Oyo ya shafa

- Sanata Rabiu Kwankwaso ya kaiwa wadanda rikicin Shasha ya rutsa da su dauki

- Jagoran Kwankwasiyyan ya yi alhinin abinda ya faru a garin na Ibadan

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bada gudunmuwan kayan abinci ga yan Arewan da rikicin Shasha a jihar Oyo ya shafa, rahoton DT.

Tsohon shugaban karamar hukumar Tarauni, Muktar Umar Yarima, ya jagorancin tawagar Kwankwasiyya zuwa Oyo ranar Juma'a domin gabatar da gudunmuwar ga shugabannin Hausawa dake jihar a madadin Sanatan.

Kayan abincin sun hada da buhun shinkafa 200, katon 200 na ruwan gora, da kuma lemun kwalta katon 200.

Yayin gabatar da kayan, Yarima yace, "Jagoranmu ya samu labarin cewa mutanen nan sun rasa muhallunsu kuma suna cikin halin kunci kuma suna bukatan taimako."

"Shi yasa jagoranmu ya bada gudunmuwar wadannan kayan abincin domin raba musu."

Yarima ya yi kira ga shuagbannin su taimakawa mutanen da suka rasa muhallansu.

DUBA NAN: Ina so na iya Turanci sosai, ‘yar shekara 50 da ta shiga JSS2 ta magantu

Kwankwaso ya bada gudunmuwan kayan abinci ga Hausawan da rikicin Shasha a Oyo ya shafa
Kwankwaso ya bada gudunmuwan kayan abinci ga Hausawan da rikicin Shasha a Oyo ya shafa Credit: @thesunnigeira
Asali: Twitter

DUBA NAN: Sheikh Gumi ya rokawa 'yan bindiga gafara daga gwamnatin tarayya

A bangare guda, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ranar Asabar ya caccaki gwamnonin kudu maso yamma, inda ya daura musu alhakin kashe-kashen da ya faru a kasuwar Shasha a Ibadan, jihar Oyo.

A cewar Lawan, gwamnonin ne suka tunzura matasan yankin wajen kaiwa yan Arewa hari.

A hirar da yayi da jaridar BBC Hausa, Lawan ya ce kiran da wasu gwamnonin kudu maso yamma keyi na korar Fulani daga yankin ya haifar da hakan.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel