Yanzun nan: Sheikh Gumi ya rokawa 'yan bindiga gafara daga gwamnatin tarayya
- A kokarinsa na shawo kan sace yaran makarantar GSSS Kagara, Gumi ya gana da 'yan fashin
- Malamin ya saurari bukatun 'yan fashin yayin da yake kira ga gwamnati da ta yafe musu laifin
- Malamin ya bayyana cewa tsoron kisa yasa 'yan fashin ke tsoron tuba daga aikata laifukan
Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba 'yan fashi da ke son yin sulhu idan har za a magance matsalar tsaro a yanzu.
Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin ganawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.
Wannan ya faru ne bayan malamin ya ziyarci sansanin wasu yan fashi da ke aiki a jihar Neja.
Ya bayyana cewa wasu korafe-korafen 'yan fashin shine ana kashe su tare da nakasa su ba da hakki ba.
KU KARANTA: Sace daliban Kagara: Sanata Shehu Sani ya aika sakon kar-ta-kwana ga gwamnan Neja
Da yake magana game da tattaunawar da ya yi yayin ziyarar sirri da ya kai wa 'yan ta'addan, Sheik Gumi ya ce akwai kyakkyawan martani daga' yan bindigar da ke rike da daliban makarantar Kagara da ma'aikatansu.
Amma bai bayyana ko an saki daliban ba.
Duk da haka, ana sa ran gwamna Abubakar Bello zai yiwa manema labarai bayani game da halin da ake ciki a yau.
KU KARANTA: Yanzun nan: 'Yan sanda sun fara sintiri da jiragen sama don gano daliban da aka sace a Kagara
A wani labarin, A jita-jita dake yawo a kafafen yada sada zumunta cewa an saki wasu dalibai da malamai na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara a jihar Neja, gwamnan jihar ya fayyace zahirin halin da ake ciki.
Gwamnan jihar ta Neja Abubakar Sani-Bello ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa an saki dalibai 27 da malamai 3 da aka sace a safiyar ranar Laraba a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng