Ina so na iya Turanci sosai, ‘yar shekara 50 da ta shiga JSS2 ta magantu

Ina so na iya Turanci sosai, ‘yar shekara 50 da ta shiga JSS2 ta magantu

- Folashade Ajayi wacce ke karatu a matsayin dalibar JSS 2 a makarantar Ilorin Grammar ta bayar da dalilin da yasa ta yin haka

- Tsohuwar mai shekaru 50 ta ce ba ta taba samun damar zuwa makaranta

- Da take ci gaba da magana, ta bayyana cewa tana son ci gaba da karatunta har zuwa matakin jami'a

A Najeriyar da muke a yau, mummunan labari ya zama abun da mutane ke ji a kullum. Amma wata tsohuwa mai shekaru 50 a Ilorin, jihar Kwara, Misis Folashade Ajayi, ta dan sauya labarin.

Ajayi, yar asalin garin Iludun-Oro a karamar hukumar Irepodun ta jihar a kokarin ta na neman ilimi ta samu kanta a matsayin dalibar JSS 2 a makarantar Ilorin Grammar School.

A cewar ta, ba ta taba samun damar zuwa makaranta ba duk da cewa ta na matukar son ilimi, jaridar Punch ta ruwaito.

Ina so na iya Turanci sosai, ‘yar shekara 50 da ta shiga JSS2 ta magantu
Ina so na iya Turanci sosai, ‘yar shekara 50 da ta shiga JSS2 ta magantu Hoto: Punch
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Bidiyon sojojin Najeriya yayin da suka kwace gonar Shekau a dajin Sambisa

Ta kara da cewa dalilinta na shiga makarantar shi ne don cika dadadden burinta da kuma iya Turanci sosai.

Ta ce:

"A koyaushe ina matukar son zuwa makaranta amma ban samu dama ba (a lokacin da nake karama). Saboda kaunar karatun da nake yi, a baya na yi karatun yaki da jalinci inda na samu takardar shaidar kammalawa. Na halarci makarantar manya a shekarar 2017. Daga nan, na yanke shawarar cigaba kuma wannan shine dalilin da ya sa na tsinci kaina a nan a yau. Na yi jarabawar kammala karatun firamare a babbar sakandaren Gwamnati, Adeta, Ilorin a shekarar 2017. Na ci jarabawar kuma an ba ni takardar shaidar kammala makarantar Firamare.

"Bayan kammala makarantar sakandare, har yanzu ina da burin zuwa makarantar jami’a saboda ina sha'awar karatun boko. Idan aka ba ni dama, zan je jami’a amma hakan ya dogara ne da yardar Allah."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: FG ba za ta biya kudin fansa don sakin daliban Kagara ba - Lai Mohammed

A wani labarin, Enoch Adejare Adeboye, wanda ya kafa kuma shugaban cocin Redeem Christians Church of God (RCCG), ya yi kira da a saki Leah Sharibu.

Sharibu, wacce ta kasance kirista mai shekaru 14 a lokacin da aka kama ta, ita kadai ce yar makarantar Dapchi da ta rage a hannun yan ta’addan bayan mamayar da Boko Haram ta kai masu a garin Dapchi da ke jihar Yobe a 2018.

An ruwaito cewa ta ki yarda ta bar addininta a lokacin da wadanda suka sace ta suka yi kokarin musuluntarta ta farkin tuwo.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel