Kisan yan Arewa a Kudu: Duk laifinku ne, Sanata Ahmad Lawan ya caccaki gwamnonin Yarbawa

Kisan yan Arewa a Kudu: Duk laifinku ne, Sanata Ahmad Lawan ya caccaki gwamnonin Yarbawa

- Sanata Ahmad Lawan ya yi tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a fadin tarayya

- Musamman, Sanata ya caccaki gwamnoni kan rashin baiwa yan Arewa kariya

- Wannan shine karo na farko da shugaban majalisar yayi magana ga gwamnonin

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ranar Asabar ya caccaki gwamnonin kudu maso yamma, inda ya daura musu alhakin kashe-kashen da ya faru a kasuwar Shasha a Ibadan, jihar Oyo.

A cewar Lawan, gwamnonin ne suka tunzura matasan yankin wajen kaiwa yan Arewa hari.

A hirar da yayi da jaridar BBC Hausa, Lawan ya ce kiran da wasu gwamnonin kudu maso yamma keyi na korar Fulani daga yankin ya haifar da hakan.

Hakazalika, yace kalaman gwamnonin ya haddasa hare-haren da ake kaiwa yan Arewa a kudancin Najeriya.

"Abinda ya faru a jihar a Oyo, da kuma abubuwan da suk adan faru a wasu jihohin kudu maso yammacin Najeriya, watakila da kudu maso gabashi, an samu matsalan shugabancin," Yace.

"Gwamnonin suke ke da hakki muhimmi don kare mutanen dake yankinsu."

"Kuma irin kalamai da wasu gwamnoni sukayi, musamman daga wannan yankin ya taimaka wajen tunzura mutanen yan asalin jihohin, wadanda ke ganin ai shugabanninsu sun basu lasisi ne."

DUBA NAN: Daliban Kagara: Ba zan biya N500m da suke nema kudin fansa ba, gwamna Niger ya jaddada

Kisan yan Arewa a Kudu: Duk laifinku ne, Sanata Ahmad Lawan ya caccaki gwamnonin Yarbawa
Kisan yan Arewa a Kudu: Duk laifinku ne, Sanata Ahmad Lawan ya caccaki gwamnonin Yarbawa
Asali: Twitter

DUBA NAN: Sheikh Gumi ya rokawa 'yan bindiga gafara daga gwamnatin tarayya

Zaku tuna cewa a ranar 18 ga Febrairu, rikici ya barke a Shasha sakamakon rashin fahimta tsakanin wasu kuma yayi sanadiyar rashin rayuka da dukiyoyi.

A bangare guda, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bada gudunmuwan kayan abinci ga yan Arewan da rikicin Shasha a jihar Oyo ya shafa, rahoton DT.

Tsohon shugaban karamar hukumar Tarauni, Muktar Umar Yarima, ya jagorancin tawagar Kwankwasiyya zuwa Oyo ranar Juma'a domin gabatar da gudunmuwar ga shugabannin Hausawa dake jihar a madadin Sanatan.

Kayan abincin sun hada da buhun shinkafa 200, katon 200 na ruwan gora, da kuma lemun kwalta katon 200.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel