Rikicin Boko Haram za ta kwashe shekaru 20 bata kare ba, Buratai

Rikicin Boko Haram za ta kwashe shekaru 20 bata kare ba, Buratai

- Karon farko, Buratai ya bayyana dalilin da yasa Soji suka gaza kawar da yan Boko Haram

- A cewarsa, rashin shugabanci na cikin abubuwan da zasu hana rikicin karewa

- Ya ce akwai wuraren da gwamnati bata san da su a Najeriya

Tsohon hafsan Sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai (mai murabus), a ranar Alhamis ya ce da yiwuwan wannan rikicin na Boko Haram ta cigaba har tsawon shekaru ashirin masu zuwa.

Ya ce da dadewa, yan ta'addan sun canza akidun mutane, kuma hakan zai sa kawo karshen yaki abu mai matukar wuya.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin da ya gurfana gaban kwamitin harkokin wajen Najeriya na majalisar dattawa domin tantanceshi matsayin Ambasada.

Tsohon Sojan ya ce duk da cewa Sojojin Najeriya na samun hadin kai daga kasashe makwabta irinsu Kamaru, Chadi da Nijar, kuma ana samun nasara, amma karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen yakin ba.

Buratai ya ce akwai matsalolin siyasa da tattalin arziki da ya kamata a magance tukunna, saboda yawancin garuruwan Arewacin Najeriya na da karancin abubuwan more rayuwa.

"Sojojinmu na hada kai da Sojin Chadi da Kamaru. Mun samu nasarori. Amma yan ta'addan sun ratsa zukatan al'umma," yace.

"Jihata Borno ce hedkwatar inda akayi masifar ratsa zukatan mutane sosai. Ba abinda zaku iya cire dare daya bane."

"Sojoji kadai ba zasu iya magance matsalan ba. Akwai matsalolin tattalin arziki da ya kamata a magance. Ya kamata akwai kayan more rayuwa, amma babu."

KU KARANTA: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa

Rikicin Boko Haram za ta kwashe shekaru 20 bata kare ba, Buratai
Rikicin Boko Haram za ta kwashe shekaru 20 bata kare ba, Buratai Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

KU DUBA: Auwal Daudawa: Na jagoranci sace yaran Kankara ne saboda Gwamna Masari ya tabo mu

"Zan iya fada muku kananan hukumomi biyar a Borno da babu hanyoyi masu kyau. Hakazalika Zamfara, Katsina da Sokoto. Akwai wurare da dama a Arewa da babu alaman gwamnati saboda babu hanyoyi da kayan jin dadi," Buratai ya kara

"Za mu kwashe shekaru 20 bamu gama yakin ba."

`Kun ji cewa tsaffin hafsoshin tsaro da shugaba Muhammadu Buhari ya zaba a matsayin sabbin jakadu sun dira majalisar dattawa don tantancesu da tabbatar da su.

Mambobin majalisar sun hana yan jarida shiga.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel