Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa
- Tubabben shugaban yan bindiga a Zamfara, Auwal Daudawa ya ce siyan bindiga a wurinsa tamkar siyan burodi ne
- Daudawa ya ce rashin adalci da jami'an tsaro da yan sa-kai suka masa ne yasa ya sayar da kadarorinsa ya siya bindiga
- Tsohon dan bindigan ya magantu kan yadda jami'an tsaro suka tattara dukkan shanun da ya mallaka a Zamfara duk da cewa babu na sata a ciki
Tsohon tubabben shugaban yan bindiga, Auwal Daudawa, ya bayyana cewa samun bindiga sauki gare shi kamar yadda ake siyan burodi.
Daudawa ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da Daily Trust.
Da aka tambaye shi yadda ya ke samun bindigu, ya ce: "Akwai su barkatai. Samun bindiga ba abu ne mai wuya ba. Kamar zuwa ne ka siya burodi."
DUBA WANNAN: Hotunan ɗalibar da ta tafi makaranta da bindiga za ta harbi malamin da ya ce ta aske gashinta mai launi
Daudawa ya ce rashin adalcin da ya fuskanta a rayuwa ne ya saka shi ya zama dan bindiga.
"Saboda rashin adalci ne. Rashin adalci kamar a ce kana da kayanka kana kulawa da iyalanka kawai sai gwamnati ta aike da jami'anta su kwashe maka dukkan abinda ka mallaka yayin da ina da iyalai da zan kula da su.
"Mai zan yi? Kasa ake tsammani zan ci? Ina ga shanu da na gada daga iyaye na amma an aiko da jami'ai sun kwace sannan suka kawo ni nan Gusau. Don haka na tunkari kallubalen."
Da rashin adalcin da ya fuskanta, Daudawu ya kara da cewa jami'an tsaro sun kwace masa shanunsa a Zamfara. Hakan yasa ya siyar da sauran abinda ya mallaka ya siya bindiga.
KU KARANTA: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'
"Jami'an tsaro ne suka aikata hakan. Ba zan iya sanin wanda ya turo su ba amma a zamanin gwamnatin da ta gabata ne (a jihar Zamfara). Jami'an tsaro da yan sa-kai (vigilante) suka kwace min shanu.
"Na ce su bincika garken idan sun ga ko shanu daya da ba nawa bane kada su raga min. Ba su samu shanun sata ba amma duk da hakan suka tafi da duka shanun. Ka fada min? Mai zan yi da rayuwa na?
"Na dogara ga Allah na dogara ga shanu na amma suka kwace min komai. Wannan ne dalilin da yasa na siyar da sauran abinda na mallaka na siya bindiga na fara fashi."
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng