Yanzu-yanzu: Buratai da sauran tsaffin hafsoshin tsaro sun dira majalisa

Yanzu-yanzu: Buratai da sauran tsaffin hafsoshin tsaro sun dira majalisa

- Shugaba Buhari ya bukaci majalisa ta amince da zaben manyan tsaffin Sojoji matsayin jakadu

- Idan majalisa ta amince, za'a turasu kasashen waje daban-daban don aikin diflomasiyya

- Buhari ya saukesu ne makkonin baya kuma ya nada sabbin hafsoshin tsaro

Tsaffin hafsoshin tsaro da shugaba Muhammadu Buhari ya zaba a matsayin sabbin jakadu sun dira majalisar dattawa don tantancesu da tabbatar da su, Vanguard ta ruwaito.

Mambobin majalisar sun fara tantancesu amma an hana yan jarida shiga.

Tsaffin hafsoshin tsaron sun dira majalisa ne misalin karfe 11:32 na safiyar Alhamis, 18 ga Febrairu, 2021.

Sun hada da Abayomi Olonisakin, Tukur Buratai, Ibok-Ete Ekwe Ibas, da Sadique Abubakar.

Isarsu ke da wuya suka shiga ofishin mai baiwa Buhari shawara kan majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare, wanda ya shigar da su dakin taro.

Daidai misalin karfe 12, shugaban kwamitin, Adamu Muhammad Bulkachuwa, ya bukaci su sanya labule da mambobin kwamitin.

Ana shiga irin wannan labule ne domin tattauna yadda za'a yi saboda gudun samun sabani gaban jama'a.

KU KARANTA: Auwal Daudawa: Na jagoranci sace yaran Kankara ne saboda Gwamna Masari ya tabo mu

Yanzu-yanzu: Buratai da suran tsaffin hafoshin tsro sun dira majalisa
Yanzu-yanzu: Buratai da suran tsaffin hafoshin tsro sun dira majalisa Credit: Presidency
Asali: Twitter

DUBA NAN: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata, 9 ga Febrairu, 2021, ya bukaci majalisar dattawan tarayya ta tabbatar da tsaffin hafsoshin tsaron Najeriya matsayin Jakadu zuwa kasashen waje.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisa ranar Talata.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng