Auwal Daudawa: Na jagoranci sace yaran Kankara ne saboda Gwamna Masari ya tabo mu

Auwal Daudawa: Na jagoranci sace yaran Kankara ne saboda Gwamna Masari ya tabo mu

- Tubabben dan bindigar da ya jagoranci sace daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kankara, Jihar Katsina, Auwal Daudawa ya bayyana dalilinsu na yin hakan

- Daudawa ya ce shi da tawagarsa sun aikata hakan ne domin nuna wa Gwamna Aminu Masari cewa suna da karfin hadassa tashin hankali a jihar

- Ya kuma bayyana cewa sun yi hakan ne saboda Masarin ya ce ba zai zauna ya tattauna da su don yin sulhun zaman lafiya ba

Auwal Daudawa, wanda ya jagoranci sace daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kankara, Jihar Katsina, ya ce ya jagoranci wannan samamen ne saboda Gwamna Bello Masari ya kuskurewa dakarunsa.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust, Daudawa ya ce ya so tabbatar wa da gwamnati cewa yana da karfin da zai kai irin wannan harin.

Ya ce Masari ya saba zabin tattaunawa da kungiyarsa kuma ya so ya nuna wa gwamnan cewa za su iya haddasa tashin hankali.

Auwal Daudawa: Na jagoranci sace yaran Kankara ne saboda Gwamna Masari ya tabo mu
Auwal Daudawa: Na jagoranci sace yaran Kankara ne saboda Gwamna Masari ya tabo mu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya ce, “Ban taba yin irin wannan satar ba a Zamfara. Na yi haka ne a Katsina saboda gwamna ya fito ya ce ba zai sake tattaunawa da mutanenmu ba. Don haka, mun ce tunda sun ce ba su da sha'awar yarjejeniyar sulhu kuma suna aika jiragen soji don azabtar da mutanenmu, da rusa abin da muke da su, ya kamata mu kai yakin ga wadanda ba sa son zaman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Gwamnan Arewa ya zargi takwarorinsa da yin sakaci da aikinsu

“Na yi hakan ne don nuna cewa ina da karfin yin hakan kuma ba na jin tsoron kowa sai Allah. Don gwamnati, da duk duniya su san cewa za mu iya yin hakan ne amma har yanzu ba muna da sha'awar aikata wani abu makamancin haka bane.”

Daudawa ya kuma musanta cewa kungiyar sa ta karbi kudin fansa kafin ta saki daliban sama da 300 da aka sace, inda ya kalubalanci duk wanda ke da wata hujja sabanin haka da yayi magana.

“Bayan satar za ku ga cewa ba ni da wahalar bayyana yayin tattaunawa saboda ban yi ta saboda kudi ba. Idan da don kudi ne, da ban sake su ba koda an bani naira tiriliyan 2. Duk duniya ta sani, idan aka ba ni kudi za a sani, idan ba a ba ni ba shima za a sani. Ba za a iya ɓoye shi ba.”

Kafin ya ajiye makamansa, Daudawa na jagorantar wata tawagar yan fashi da ke zama a dajin Dumburum a karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara.

Tawagarsa na addabar mazauna yankin da masu amfani da hanyoyin a Zurmi-Gidan Jaja da Jibia da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: Siyasa ce ke rura wutar ta’addanci a Najeriya, Farfesa Taufiq AbdulAziz kan sace daliban Kagara

A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ba duka tsagerun yan bindiga bane mutanen banza, wasu kawai dole ce ta wajabta musu daukar bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 18 ga Febrairu, 2021, Vanguard ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa yawancin yan bindigan sun shiga harkar ne saboda irin rashin adalcin da al'ummar gari ke musu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng