Sace Daliban Kagara: Diyar Babangida ta bayyana abubuwa 4 da suka janyo hakan

Sace Daliban Kagara: Diyar Babangida ta bayyana abubuwa 4 da suka janyo hakan

- Aisha Babangida ta bayyana cewa cin hanci da rashawa na cikin abubuwan da ya haddasa sace daliban Kagara

- A tsokacin da tayi, Aisha Babangida tace ji take tamkar ita aka sace lokacin da ta samu labarin

- Ta yi addu'an Allah ya bayyana daliban su koma wajen iyalansu cikin koshin lafiya

Aisha Babangida, diyar tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Babangida ta yi kira ga gwamnatin tarayya tayi dubi cikin asalin abubuwan da suka haddasa sace-sacen mutane.

A jawabin da ta saki a shafinta na Instagram ranar Alhamis, 18 ga Febrairu, Aisha ta yi Alla-wadai da sace daliban makarantar GSC Kagara.

Ta yi addu'an Allah ya sa a gano yaran cikin koshin lafiyansu inda tace tana ji tamkar ita aka sace.

Legit Hausa ta ruwaito muku yadda wasu yan ta'adda a ranar Talata, 16 ga Febrairu, suka dira makarantan gwamnatin GSC Kagara suka kashe dalibi daya, suka sace dalibai da malamai.

Wannan ya biyo bayan sace daliban Makarantan Sakandare a garin Kankara, jihar Katsina.

Aisha Babangida tace talauci, jahilci, son kai da rashawa ne manyan ummul haba'isin sace-sacen mutane a Najeriya.

Sace Daliban Kagara: Diyar Babangida ta bayyana abubuwa 4 da suka janyo hakan
Sace Daliban Kagara: Diyar Babangida ta bayyana abubuwa 4 da suka janyo hakan Credit: Aisha I. Babangida
Asali: Instagram

Tace: "Na ji kama ni aka sace lokacin da na samu labarin sace yaranmu a makarantar gwamnatin GSC Kagara, jihar Neja."

"Sace mutane aikin shaidanu ne.... Ina addu'a an gani yaran nan cikin lokaci."

"Abubuwan dake ja ana satan mutane basu wuce rashin aikin yi ba, talauci, jahilci, son kai da rashawa."

DUBA NAN: Fargaba ya cika Neja bayan masu satar mutane sun saki bidiyon matafiyan da aka sace, sun nemi a biya N500m

DUBA NAN: Majiya ta shaida yadda aka sace dalibai da malaman GSSS Kagara

A bangare guda, daya daga cikin sanatocin jihar Sani Musa (Neja ta Gabas) ya ce wadanda suka aikata garkuwan ‘yan ta’adda ne, ba’ yan fashi ba kamar yadda ake zato.

Da yake magana da Channels TV a ranar Laraba, 17 ga watan Fabrairu, Musa ya misalta mummunan satar da aka yi da na Chibok (Borno), Dapchi (Yobe) da Kankara (Katsina).

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel