Majiya ta shaida yadda aka sace dalibai da malaman GSSS Kagara
- A binciken yadda lamarin sace daliban Kagara, mun gano yadda lamarin ya faru
- Wata majiya ta shaida yadda aka sace malaman makarantar kafin azo kan daliban
- Hakazalika barayin sun boye baburansu, kafin daga bisani suka far wa makarantar
Wani mazauni da ya shaida yadda aka sace dalibai 27 da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati 15, Kagara da ke cikin Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja, ya bayyana yadda masu garkuwar suka daure wadanda suka sace su bibbiyu suka tafi da su.
Mutumin, wanda ke zaune kusa da makarantar, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa ‘yan fashin, wadanda ke sanye da kayan sojoji, sun far wa makarantar da karfe 2 na dare.
Majiyar Legit.ng Hausa ta lura cewa gine-gine da yawa da suka hada da azuzuwa da dakunan kwanan dalibai sun lalace.
Majiyar, wacce ta bayyana yadda lamarin ya faru, ta bayyana cewa kafin su koma GSS Kagara, ‘yan fashin sun ajiye babura kusa da makarantar Sakandiren Attahiru, mai nisan kilomita daya zuwa GSS Kagara.
KU KARANTA: Buhari ya tura jami'an tsaro jihar Neja don su kwato daliban da aka sace
Ya ce, "Lokacin da (wadanda aka kwashe din) aka dauke su, sai na ga an daure su biyu-biyu sannan suka doshi inda aka ajiye babura daga inda aka dauke su zuwa daji."
Wani ma’aikacin makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa majiya cewa ‘yan bindigar sun shiga makarantar ne daga baya, inda shingen ya fadi.
A cewarsa, sun nufi rukunin ma’aikata, inda aka yi garkuwa da ma’aikata 15, ciki har da malamai kafin su tafi dakin kwanan dalibai.
A cewar wata majiyar Punch, wani babban dalibin makarantar sakandare na aji 3, Bejamin Abila, shine ya ankarar da jama'a lokacin da 'yan bindigar ke gab da gidan kwanan dalibai cewa an sacesu.
“Sun yi awon gaba da dalibai 27 a cikin dakin kwanan dalibai tare da daure dukkanin wadanda aka sace din biyu-biyu kafin su dauke su daga makarantar,” in ji majiyar.
Wata majiyar ta koka da yadda makarantar ta lalace, tana mai cewa tana fuskantar hare-haren ‘yan fashi.
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Bazan biya kudin fansa ba ko kobo, Gwaman Neja
A wani labarin, Majalisar dattijai, a ranar Laraba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da, cikin gaggawa, ya sanya dokar ta baci kan tsaro sakamakon sace ma’aikata da dalibai a wata makaranta a Niger.
Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Muhammed Sani Musa (APC, Neja) ya gabatar wanda ya ja hankalin abokan aikinsa kan sace wasu dalibai da ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, Jihar Neja, da misalin karfe 2 na daren Laraba.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng