Daliban Kagara: Ba 'yan fashi bane - Tsoro ya mamaye Neja yayin da sanata ya bayyana asalin masu satar mutane

Daliban Kagara: Ba 'yan fashi bane - Tsoro ya mamaye Neja yayin da sanata ya bayyana asalin masu satar mutane

- Sanata Sani Musa ya ce ‘yan ta’adda ne ke da alhakin sace daliban kwaleji a Kagara

- Dan majalisar mai wakiltar Neja ta Gabas ya kwatanta satar da na Dapchi, Chibok da Kankara

- Musa ya yi gargadin cewa dole ne hada karfi da karfe saboda irin wannan lamarin na iya faruwa a wata jihar

Sa’o’i kadan bayan sace daliban Kagara na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Neja, daya daga cikin sanatocin jihar Sani Musa (Neja Gabas) ya ce wadanda suka aikata garkuwan ‘yan ta’adda ne, ba’ yan fashi ba kamar yadda ake zato.

Da yake magana da Channels TV a ranar Laraba, 17 ga watan Fabrairu, Musa ya misalta mummunan satar da aka yi da na Chibok (Borno), Dapchi (Yobe) da Kankara (Katsina).

Legit.ng ta lura cewa 'yan fashi sun yi ta aiwatar da sace-sacen mutane a fadin kasar a yayinda ake tsaka da fama da rikice-rikicen tsaro wanda hakan ya tilasta gwamnatin tarayya canza shugabannin hafsoshin tsaro a watan Janairu.

Daliban Kagara: Ba 'yan fashi bane - Tsoro ya mamaye Neja yayin da sanata ya bayyana asalin masu satar mutane
Daliban Kagara: Ba 'yan fashi bane - Tsoro ya mamaye Neja yayin da sanata ya bayyana asalin masu satar mutane Hoto: @MSMusa313
Asali: Twitter

Wannan wallafar ya kuma lura da cewa, Neja ta zama sabon sansanin wasu gungun 'yan fashi da masu satar mutane, inda Amurka ta kuma yi gargadin cewa' yan ta'addan Boko Haram suna cikin jihar a halin yanzu.

KU KARANTA KUMA: Fargaba ya cika Neja bayan masu satar mutane sun saki bidiyon matafiyan da aka sace, sun nemi a biya N500m

A ranar Talata, 16 ga Fabrairu, wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun afka wa kwalejin gwamnati, suka yi ta harbi ba kakkautawa tare da kashe wani dalibi da kuma sace wasu da dama ciki har da malamai.

Da yake martani kan lamarin, Musa ya yi gargadin cewa dole ne gwamnati ta kara kaimi kan ayyukan 'yan fashi da' yan ta'adda saboda babu wanda ya san wasu makarantu za a kaiwa hari a gaba.

Dan majalisan ya ce:

“Babu kowa a wurin sai 'yan fashin. Ba na kiransu ’yan fashi, ina kiransu da ’yan ta’adda.

"Ya faru a Chibok, ya faru a Dapchi, ya faru a Kankara, ya faru a Kagara, ba za mu iya tabbatar da ina ne na gaba ba, don haka, dole ne a dauki matakan da suka dace."

KU KARANTA KUMA: 2023: PDP tayi magana kan zargin tsayar da Atiku da kuma tsige shugabanta na kasa

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yammacin ranar Laraba, 17 ga watan Fabrairu, ya gana da gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, a fadar Shugaban kasa kan sace ‘yan makarantar sakandaren gwamnati da ke Kagara.

‘Yan fashin sun sace dalibai 27, ma’aikata uku da wasu‘ yan uwa a makarantar a safiyar ranar Laraba.

Bayan ganawar, Gwamna Bello ya shaida wa manema labarai cewa ya yi magana da shugaban kasa kan tura karin jami’an tsaro zuwa jihar, da kuma aiki don tabbatar da dawwamammen maslaha a kan rashin tsaro, jaridar The Cable ta ruwaito.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel