Fargaba ya cika Neja bayan masu satar mutane sun saki bidiyon matafiyan da aka sace, sun nemi a biya N500m

Fargaba ya cika Neja bayan masu satar mutane sun saki bidiyon matafiyan da aka sace, sun nemi a biya N500m

- An yi garkuwa da matafiya da yawa a jihar Neja a yayinda ake tsaka da fama da matsalar rashin tsaro a kasar

- Wadanda suka sace su suna neman gwamnati ta basu zunzurutun kudi har Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansa

- Kungiyar yan ta’addan ta saki wani faifan bidiyo na matafiyan suna rokon gwamnati da ta ceto su

A wani dan cikas da aka samu a kokarin da ake na magance matsalar rashin tsaro a kasar, wasu da ake zargin 'yan fashi ne sun sace matafiya da dama a jihar Neja.

An yi garkuwa da matafiyan ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Fabrairu, a kan wata babbar hanya, inda rahotanni suka nuna cewa masu garkuwar sun nemi a ba su kudi har Naira miliyan 500 kafin su sake su.

Wata kungiyar yan ta’adda ta saki bidiyon matafiyan suna rokon gwamnati da ta kwato musu yanci a ranar Talata, 16 ga Fabrairu.

Fargaba ya cika Neja bayan masu satar mutane sun saki bidiyon matafiyan da aka sace, sun nemi a biya N500m
Fargaba ya cika Neja bayan masu satar mutane sun saki bidiyon matafiyan da aka sace, sun nemi a biya N500m Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Legit.ng ta lura cewa 'yan fashi sun yi ta aiwatar da sace-sacen mutane a fadin kasar a yayinda ake tsaka da fama da rikice-rikicen tsaro wanda hakan ya tilasta gwamnatin tarayya canza shugabannin hafsoshin tsaro a watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Arewa ga mutanen Arewa: Kada ku kai wa ‘yan kudu hari a arewa

Wannan wallafar ya kuma lura da cewa, Neja ta zama sabon sansanin wasu gungun 'yan fashi da masu satar mutane, inda Amurka ta kuma yi gargadin cewa' yan ta'addan Boko Haram suna cikin jihar a halin yanzu.

Kwanakin baya, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi wa matafiya kwanton bauna wadanda ke dawowa daga daurin aure a karamar hukumar Rijau da ke jihar.

A cewar Jaridar Premium Times, wani jami'in kungiyar NURTW a Tegina, Bello Muhammed, ya tabbatar da ci gaban.

Mohammed ya kuma kara da cewa an kashe wasu mambobin kungiyar tsaro guda 3 da suka yi yunkurin dakile satar a nan take.

Daga baya wata jami’ar gwamnati, Mary Berje, ta tabbatar da cewa “10 daga cikin fasinjojin da aka sace kwanan nan a cikin motar Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja da ke komawa Minna daga karamar Hukumar Rijau sun samu yanci.“

Wani faifan bidiyo na matafiya ya bayyana yanzu haka kuma an ga daya daga cikin ‘yan bindigar da ya yi magana da harshen Hausa yana yi wa wadanda abin ya shafa bayanin abin da za su fada.

KU KARANTA KUMA: Malami ya shawarci FG da ta kirkiro hukumar kula da ayyukan makiyaya

A wani labarin, Gwamna Sani Bello na jihar Niger ya bada umurnin rufe makarantun kwana da ke wasu kananan hukumomi hudu na jihar nan take, Daily trust ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan sace wasu dalibai da ma'aikatan makarantar kwallejin Kimiyya ta gwamnati da ke Kagara.

Yan bindiga sun afka makarantar a daren ranar Talata sun sace dalibai da kuma wasu ma'aikatan makarantar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411`

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel