COVID-19: NAFDAC ta amince a fara yi wa 'yan Nigeria amfani da rigakafin AstraZeneca

COVID-19: NAFDAC ta amince a fara yi wa 'yan Nigeria amfani da rigakafin AstraZeneca

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nigeria, NAFDAC, ta amince a fara amfani da rigakafin korona na AstraZeneca a kasar

- Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta kafa kwamiti na musamman da ya yi nazari kan ingancin rigakafin ya kuma tabbatar da dacewarsa ga yan Nigeria

- Shugaban NAFDAC, DR Mojisola Adeyeye ta ce hukumar na cigaba da nazarin wasu rigakafin har ma da magunguna na gargajiya na korona

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nigeria, NAFDAC, ta amince da ingancin allurar rigakafin annobar korona na kamfanin Oxford/AstraZeneca don yin amfani da shi a kasar, Channels Television ta ruwaito.

Shugaban hukumar NAFDAC, Dakta Mojisola Adeyeye ce ta sanar da hakan yayin jawabin da ta yi kai tsaye a ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'

COVID-19: NAFDAC ta amince a fara yi wa 'yan Nigeria amfani da rigakafin AstraZeneca
COVID-19: NAFDAC ta amince a fara yi wa 'yan Nigeria amfani da rigakafin AstraZeneca. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

Ta ce ana iya ajiye allurar rigakafin a yanayin sanyi na centigrade 2 zuwa 8.

A cewar shugaban na NAFDAC, akwai wasu rigakafin da aka yin nazari a kansu a yanzu amma nazarin da aka yi kan Astrazeneca ya nuna cewa yana maganin kwayar cutar samfurin UK da aka gano a Nigeria.

KU KARANTA: Haramta wa'azi: Abduljabbar ya roƙi lauyoyi su janye ƙarar da suka shigar kan Ganduje

Dr Adeyeye ta ce kawo yanzu ba a samu kwayar cutar samfurin kasar Afrika ta Kudu a Nigeria ba, inda ta kara da cewa ana nazari kan wasu magungunan gargajiya da za a iya amfani da su don yakar korona.

A baya-bayan nan ne Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta amince da a rika amfani da allurar da AstraZeneca ga wadanda ke bukatar rigakafi na gaggawa. NAFDAC ta ce ta karbi allurar rigakafin nata a makon da ta gabata kuma ta kafa kwamiti domin nazarin ingancinsa da dacewarsa ga yan Nigeria.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel