Haramta wa'azi: Abduljabbar ya roƙi lauyoyi su janye ƙarar da suka shigar kan Ganduje

Haramta wa'azi: Abduljabbar ya roƙi lauyoyi su janye ƙarar da suka shigar kan Ganduje

- Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya roki lauyoyin da suka yi karar gwamnatin Kano da Ganduje a madadinsa su janye

- Sheikh Abduljabbar ya ce a ganinsa ya kamata a dakata da batun kotu tunda har yanzu gwamnatin jihar ba ta kammala bincike kan zargin da ake masa ba

- Malamin ya mika godiya ga lauyoyin da suka shigar da kara saboda kauna da damuwa da suka yi da halin da ya shiga inda ya ce yana fatan za a yi masa adalci a binciken

Malamin addinin musulunci a jihar Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya roki dukkan lauyoyin da suka yi karar gwamnatin Kano da gwamna Abdullahi Ganduje a madadinsa su janye karar, Daily Trust ta ruwaito.

Abduljabbar, cikin wata gajeruwar bidiyo da ya raba wa manema labarai a Kano a ranar Laraba ya ce ya yi wannan kirar ne saboda yana ganin ya kamata a bari gwamnatin ta kammala bincike kan lamarin.

Babban malamin, a ranar Laraba da ta gabata ya tafi babban kotun jihar Kano inda ya ke neman kotun ta janye haramcin da aka masa na yin wa'azi da kuma bude makarantarsa da aka rufe.

DUBA WANNAN: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano

Haramta wa'azi: Abduljabbar ya roki lauyoyi su janye karar da suka shigar kan Ganduje
Haramta wa'azi: Abduljabbar ya roki lauyoyi su janye karar da suka shigar kan Ganduje. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa malamin yin wa'azi a jihar kan zargin cewa yana yin wa'azi da karatun za su iya harzuka mutane.

Gwamnatin ta bada umurnin rufe dukkan wuraren da malamin ke karatu a jihar har zuwa lokacin da hukumomin tsaro za su kammala bincike a kansa.

Shaihin ya roki gwamnati ta yi adalci a binciken da ake masa.

KU KARANTA: Fusatattun dandazon mutane sun lalata gidan mataimakin gwamnan jihar Niger

Ya ce, "A shirye na ke in amsa sakamakon binciken muddin anyi gskiya da adalci.

"Babu bukatar zuwa kotu idan an yi adalci. Mu jira gwamnati tukuna.

"Wannan shine dalilin da yasa na ke rokon lauyoyi su janye kararrakin saboda ina kyautata zaton za a yi adalci a binciken."

Malamin ya kara da cewa, "Masu tausaya wanda wasun su lauyoyi ne suka shigar da dukkan kararrakin. Ina rokon su kwantar da hankalinsu.

"Na san sun damu shi yasa suka aikata abinda suka yi.

"Ina godiya amma ina fatan za su amince da abinda na roka su kuma aiwatar.

"Don haka, ina son mika godiya ta garesu bisa goyon baya, kauna da damuwa kan halin da na shiga."

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel