Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'

Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'

- Wata tsohuwar sarauniyar kyau a kasar Romania ta rasa aikinta saboda tsabar kyawun da ta ke da shi

- Claudia Aredelean mai shekaru 27 ta wallafa sanarwar cewa asibitin ya nada ta mukami a kwamitinsa a dandalin sada zumunta

- Hakan ya yi sanadin mutane suka rika sukarta da cewa saboda kyanta aka nada ta hakan ya janyo asibitin ta umurci ta yi murabus

An umurci wata tsohuwar sarauniyar kyau ta yi murabus daga aikinta a asibiti saboda 'kyan ta ya yi yawa' kamar yadda LIB ta ruwaito.

An nada Claudia Ardelean, mai shekaru 27 ta yi aiki a kwamitin asibitin Pneumophthisiology Clinical Hospital a kasar Romania duk da cewa ba za a rika biyanta albashi ba.

Ardelean tana da digiri biyu a aikin lauya da nazarin al'adun turawa.

Sarauniyar kyau ta rasa aikinta a asibiti saboda 'kyawunta ya yi yawa'
Sarauniyar kyau ta rasa aikinta a asibiti saboda 'kyawunta ya yi yawa'. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

Bayan samun aikin, ta yi farin ciki har ta wallafa a kafar sada zumunta a ranar 8 ga watan Fabarairu.

DUBA WANNAN: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano

Tsohuwar sarauniyar kyan ta wallafa hoton selfie da ta dauka a gaban ginin asibitin inda ta rubuta: "Ina godiya saboda gudunmawa da amintaka da na samu daga Cluj Nationtal Liberal Party!".

Sarauniyar kyau ta rasa aikinta a asibiti saboda 'kyawunta ya yi yawa'
Sarauniyar kyau ta rasa aikinta a asibiti saboda 'kyawunta ya yi yawa'. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

Sai dai bayan hakan, wasu suka fara sukar ta suna cewa ta samu aikin ne kawai saboda kyau da ta ke da shi.

Newspaper Click ya ce sakamakon sukar da aka yi mata, an tilasta mata yin murabusa saboda tana da "kyau da yawa".

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari GSC Kagara a Niger, sun kashe dalibi daya sun sace wasu

Claudia wacce yanzu ta ke aiki a matsayin lauya a wani kamfanin kasar ba ta yi tsokaci game da ajiye aikinta na kwamitin asibitin ba.

Shugaban Cluj Alin Tise ta amsa cewa ta cancani amma duk da hakan ta fitar da sanarwa cewa, "na yi nadamar abinda ya faru.

"Na bukaci Claudia Ardelean ta yi murabus."

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel