Ana rade-radin cewa wasu kusoshi na yunkurin tunbuke Shugaban jam’iyyar PDP na kasa

Ana rade-radin cewa wasu kusoshi na yunkurin tunbuke Shugaban jam’iyyar PDP na kasa

- Jita-jita na yawo cewa kujerar Prince Uche Secondus ta na girgidi a PDP NWC

- Kola Ologbondiyan ya ce babu wadanda su ke neman tsige shugaban jam’iyya

- Mai magana da yawun PDP ya ce kalau NWC ta ke da Shugaba Uche Secondus

Jam’iyyar PDP ta fito ta yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa majalisar NWC ta na kiran a sauke Prince Uche Secondus.

Jaridar The Nation ce ta rahoto sakataren yada labaran PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya na cewa babu wani yunkuri da ake yi na tsige shugaban na su.

Da yake magana a gaban manema labarai a ranar Laraba, 17 ga watan Fubrairu, 2021, Ologbondiyan ya tabbatar da cewa kan NWC a hade yake.

Mista Ologbondiyan yake cewa: “Mu na da nauyi a kanmu na tafiyar da jam’iyya zuwa gaba, saboda haka ba mu da matsala da shugaban jam’iyya na kasa.”

KU KARANTA: Sanatan APC ya ce Gwamnatin Buhari ta gaza

Ya ce: “Za ku yarda da ni cewa idan har akwai wata matsala, da lamarin ba zai zama haka ba.”

Mai magana da yawun jam’iyyar adawar kasar ya zargi APC da neman kawo masu rabuwar kai, amma ya ce wannan ba zai hana su karbe mulki a 2023 ba.

“Jam’iyyar APC ce ta ke kokarin raba kan PDP. Amma tabbaci guda da zan ba ku shi ne, majalisar aiwatar wa ta NWC a dunkule ta ke.” Inji jigon ‘yan hamayyar.

“Babu sabani, kuma mu na kokarin yadda za mu kai jam’iyya ga nasara a babban zabe na 2023.”

KU KARANTA: Dalilinmu na cewa sai Buhari ya tsige Lai Mohammed – Matasan APC

Ana rade-radin cewa wasu kusoshi na yunkurin tunbuke Shugaban jam’iyyar PDP na kasa
Mr. Kola Ologbondiyan Hoto: Official Kola
Source: Facebook

A daidai wannan lokaci ne kuma kwamitin Bukola Saraki ya ke gana wa da manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP domin dinke duk wata baraka da za ta bullo.

A cikin makon nan ne mu ka tattaro maku jerin wasu manyan 'yan siyasar da suka shiga jam'iyyar APC daga makon da ya gabata zuwa 'yan kwanakin nan.

Idan za ku tuna a ranar Talata ne PDP ta yi rashin babban jigonta, kuma na-hanmun-daman Atiku, Otunba Gbenga Daniel OGD, wanda ya koma jam'iyyar APC.

Irinsu Blessing Onuh, 'diyar Sanata David Mark duk sun sauya-sheka zuwa jam'iyyar ta APC.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel