Jerin manyan mutanen da suka shiga jam'iyyar APC cikin mako guda
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Talata, 16 ga Febrairu, ta yi rashin babban jigonta, Gbenga Daniel, wanda ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Ko shakka babu, APC ta samu gagarumin karuwa sakamakon shirin sabunta rijistan zama dan majalisar.
Legit Hausa ta tattaro muku jerin mutanen da suka shiga jam'iyyar APC cikin mako guda - watanni bayan shigar gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi.
DUBA NAN: Faransa ga Afirka ta Yamma: Ku kara kaimi wajen yaki da 'yan ta'adda
1. Iyiola Omisore
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, kuma dan takaran gwamnan jihar, Iyiola Omisore, a ranar Litinin, 15 ga Febrairu, ya alanta komawarsa jam'iyyar APC daga SDP.
2. Blessing Onuh
Blessing Onuh, diyar tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, ta koma APC daga All Progressive Grand Alliance (APGA).
KU DUBA: Ba mu da niyyar kara farashin man fetur yanzu, Kamfanin NNPC
3. Yakubu Abdullahi
Alhaji Abdullahi, dan majalisar wakilan tarayya, ya koma jam'iyyar APC daga PRP ranar Laraba.
4. Gbenga Daniel
Tsohon shugaban kamfen Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2019, Gbenga Daniel, ya koma APC daga PDP ranar Talata.
Tsohon gwamnan wanda akafi sani da OGD ta yi rijista da jam'iyyar.
5. Azubuike Ihejirika
Tsohon shugaban Sojojin kasa, Laftanan Janar Azubuike Ihejirika (mai murabus) a ranar Talata ya sanar da shigarsa jam'iyyar APC.
Azubuike Ihejirika ya jagoranci sojin Najeriya tsakanin 2010 zuwa 2014 karkashin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng