Rikicin APC: Matasa sun bukaci Buhari ya sauke Lai Mohammed, ko su kore shi daga Jam’iyya

Rikicin APC: Matasa sun bukaci Buhari ya sauke Lai Mohammed, ko su kore shi daga Jam’iyya

- Wasu matasa da su ka fito daga cikin APC su na adawa da Lai Mohammed

- APC Youth Stakeholders ta zargi Lai Mohammed da kawo rudani a Kwara

- Kungiyar ta ce za ta fitar da Lai daga APC idan har ba a kore shi daga ofis ba

Wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na shiyyar kudancin jihar Kwara su na neman shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige Alhaji Lai Mohammed.

Wadannan ‘ya ‘yan jam’iyya da su ka fito karkashin lemar APC Youth Stakeholders, su na kiran a sauke Ministan tarayyar daga mukaminsa ne domin ba ya aiki.

Shugaban wannan tafiya, Tiamiyu Mumini, ya bayyana haka a madadin sauran ‘ya ‘yan APC Youth Stakeholders, ya ce bai kamata a bar Mohammed a ofis ba.

Tiamiyu Mumini ya ce Ministan al’adu da labaran kasar kansa kurum ya sani, don haka ‘ka da a bar shi ya cigaba da son kansa a maimakon yi wa kasa hidima.’

KU KARANTA: Kwara: Shugaban APC ya zargi mutanen Gwamna da hayar tsageru

“Wannan mutum ne da ya zagaye kansa da hadiman da ba daga Kwara su ka fito ba. Ya yi taurin-kai, ya ki zaben mutanen Kwara a matsayin masu ba shi shawara.”

Mumini ya ce kunnen-kashin Ministan ya hana ya fahimci yadda abubuwa su ke tafiya a jiharsa.

“Mu na so a sauke shi ne saboda ba zai yiwu ace ‘dansa ya na majalisar dokokin jihar Legas ba, amma shi ya na ci da rayuwar matasan jihar Kwara.” Inji Mumini.

Kungiyar APC Youth Stakeholders ta zargi Ministan da jawo rikici a jam’iyyar APC a Kwara, sannan ta ce Lai ba ya tare da gwamnatin AbdulRahman AbdulRazaq.

KU KARANTA: Lai Mohammed ya bukaci a soke sabunta rajistar 'yan APC a Kwara

Rikicin APC: Matasa sun bukaci Buhari ya sauke Lai Mohammed, ko su kore shi daga Jam’iyya
Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed
Source: Original

Mumini ya ce: “Mu na yunkurin dakatar da Lai daga APC na sukar aikin rajistar jam’iyya da ake yi, wanda mutane fiye da 100, 000 a mazabu 193 ne su ka yi rajista.”

"Idan Muhammadu Buhari ya ki cire shi daga Minista, za mu kore shi daga jam’iyyar APC."

Kwanakin baya kun samu rahoto cewa Ministocin Kwara biyu da ke gwamnatin Muhammadu Buhari; Lai Mohammed da Gbemisola Saraki ba su tare da APC ta jihar.

Lai Mohammed da Gbemisola Saraki sun huro wa AbdulRahman AbdulRazaq wuta. Shi kuma mai girma Gwamna, ba ya tare da bangaren Bashir Bolarinwa na APC.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel