Yanzun nan: Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza, inji sanatan APC

Yanzun nan: Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza, inji sanatan APC

- Sanata mai wakiltar Neja ta kudu, Bima Enagi, ya soki gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Bima wanda ya kasance sanatan jam'iyyar APC, ya ce gwamnatinsa ta gaza ta bangaren tsaro a kasar

- Yana martani ne a kan sace daliban makarantar sakandare na kimiya ta gwamnati, Kagara da aka yi

Bima Enagi, sanata mai wakiltar Neja ta kudu, ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nuna gazawa wajen magance matsalar rashin tsaro.

Enagi ya fadi hakan ne a zauren majalisar dattijai a ranar Laraba yayin da yake bayar da gudummawarsa ga wata muhawarar kan kudirin da Mohammed Sani Musa, sanata mai wakiltar gabashin Niger ya gabatar.

Musa ya ja hankalin takwarorinsa a kan sace wasu daliban makarantar sakandare da ke Kagara, da yan bindiga suka yi a jihar Neja.

Yanzun nan: Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza, inji sanatan APC
Yanzun nan: Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza, inji sanatan APC Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun kwashe daliban ne a sanyin safiyar ranar Laraba.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Tsohon Shugaban kasa ya yi martani a kan tashin hankalin da ke kasar

Sanatan ya ce ‘yan majalisar sun sha tattauna lamarin rashin tsaro a lokuta da dama amma maimakon abubuwa su inganta, sai kara tabarbarewa suke yi.

"Kamar yadda ɗan'uwana ya ba da rahoto, da sanyin safiyar yau 'yan ta'adda sun je wata makarantar sakandare sannan suka yi awon gaba da ɗalibai," in ji shi.

“Makiyan Allah,‘yan fashi, ‘yan ta’adda, masu satar mutane suna ko'ina. Ina zamu dosa a kasar nan? Me kuma muke bukata a matsayinmu na ‘yan majalisa da ba mu yi? Shin za mu iya cewa gwamnati ta gaza? saboda an tattauna wannan batun a kai a kai kuma babu wani ci gaba.

“Abin yana ta’azzara, na tabbata kowa a nan yana da labaran da zai bayar game da matsalolin tsaro. Me kuma ya kamata mu yi wanda ba mu yi ba? Shin ya kamata mu gyara dokokin kasar nan dan baiwa kowane dan kasa 'yancin daukar makamai?

KU KARANTA KUMA: Budurwa ta kalubalanci mutane da su shiga gasar rubutu mai kyau, ta wallafa hoton littafinta

“Shin za mu yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don bai wa gwamnoni wadanda su ne shugabannin tsaro a jihohinsu mabanbanta karin iko ne saboda gwamnatinmu wacce it ace a tsakiya tana nuna gazawa wajen magance rashin tsaro saboda ba dansa ko’ yarsa aka sace ba.

"Ina tsammanin kowa a cikin gwamnati zaiyi tunani irin wannan."

A gefe guda, mun ji cewa a yanzu haka, babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Mohammed Babagana Monguno, Shugaban yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, suna a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Sauran tawagar sune ministan labarai, Lai Mohammed da takwaransa na harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi.

Wannan yana daga cikin kokarin da gwamnatin tarayya ke yin a ceto yaran kwalejin kimiya ta gwamnati, Kagara wanda yan bindiga suka sace a daren jiya Talata, 16 ga watan Fabrairu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel