Gwamnoni 5 sun yi wa Gbenga Daniel maraba da shigowa APC

Gwamnoni 5 sun yi wa Gbenga Daniel maraba da shigowa APC

- Gwamnonin jam'iyyar APC guda biyar sun yi wa Gbenga Daniel maraba zuwa jam'iyyar APC a daren ranar Talata 16 ga watan Fabrairu

- Gwamnonin sune Abiodun na jihar Ondo; Rotimi Akeredolu na Ondo, Atiku Bagudu na Kebbi, Abdullahi Ganduje na Kano da Abubakar Sani-Bello na Niger

- Gwamna Abubakar Sani-Bello na Niger ne ya mika tsintsiya ga Gbenga Daniel da ke nuna ya shigo jam'iyyar a hukumance

An yi wa tsohon gwamnan jihar Ogun Otunba Gbenga Daniel maraba da shigowa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a daren ranar Talata, The Nation ta ruwaito.

Daniel wanda ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas a karkashin jam'iyyar PDP ya yi murabus daga jam'iyyar a Maris din 2019 bayan aiki a matsayin shugaban kungiyar yakin neman zaben shugabancin kasa na Atiku Abubakar a 2019.

Gwamnoni 5 sun yi wa Gbenga Daniel maraba da shigowa APC
Gwamnoni 5 sun yi wa Gbenga Daniel maraba da shigowa APC. Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

KU KARANTA: Sheikh Gumi: A wurin tsagerin Niger Delta ƴan bindiga suka koya satar mutane

Yayin zaben da ta gabata, Daniel ya goyi bayan Dapo Abiodun, dan takarar APC kuma ya bukaci magoya bayansa su zabe shi.

A daren ranar Talata a garinsa na Asoludero da ke Sagamu, gwamonin APC biyar sun yi masa maraba da shigowa jam'iyyar APC.

Gwamnonin sun hada da Gwamna Abiodun na jihar Ondo; Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu, Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu, Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da Gwamnan Niger, Abubakar Sani-Bello.

KU KARANTA: Umar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda ɓatanci a Kano ya bar Nigeria

Bello, wanda shine shugaban kwamitin rajista da sabunta rajistan APC ya gabatarwa Gbenga tsintsiya, alamar APC wacce ke nuna an karbe shi a jam'iyyar a hukumance.

Bello ya kuma ce Shugaban riko na APC na kasa Gwamna Mai Mala Buni zai gabatar da Daniel ga Shugaba Muhammadu Buhari nan gaba.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel