Umar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda ɓatanci a Kano ya bar Nigeria

Umar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda ɓatanci a Kano ya bar Nigeria

- Umar Faruk, matashin da aka yanke wa hukunci saboda zargin yin kalaman batanci ga Allah SWT a Kano ya fice daga Nigeria

- Piotr Cywinski, shugaban gidan ajiyar kayan tarihi na Auschwitz-Birkenau Memorial and Museum da ke Poland ne ya sanar da hakan

- Cywinski, ya ce an dauke Faruk daga Nigeria bayan sakinsa daga gidan yari ne saboda fargabar hatsarin da rayuwarsa ke ciki

- Sanarwar da Piotr Cywinski ya fitar ta ce za a sama wa Faruk muhalli da wasu ababen da zai fara sabuwar rayuwa tare da biya masa kudin makaranta

Matashi dan Najeriya Omar Faruk da wata kotun shari'a a jihar Kano ta yanke wa hukunci saboda samunsa da laifin yin kalaman batanci ga Allah SWT ya koma kasar waje saboda barazana ga rayuwarsa, The Guardian ta ruwaito.

A yanke masa hukuncin shekaru 10 a gidan gyaran hali na bayan zarginsa da amfani da kalaman da ake yi wa kallon batanci ne cikin wata hira da ya yi da abokinsa a lokacin yana da shekaru 13.

An yanke masa hukuncin ne a shekarar 2020.

DUBA WANNAN: Wasu sarakunan yankin Yarbawa na aiki tare da makiyaya da ke garkuwa, Sanata Fadahunsi

Omar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda batanci a Kano ya bar Nigeria
Omar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda batanci a Kano ya bar Nigeria. Hoto: @guardian.ng
Asali: Twitter

Sai dai wani lauya mai kare hakkin bil-adama mazaunin Legas, Kola Alapini, ya daukaka kara kan hukuncin da kotun gwamnatin Kano ta yanke masa.

Piotr Cywinski, shugaban gidan ajiyar kayan tarihi na Auschwitz-Birkenau Memorial and Museum da ke Poland shima ya roki shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya yi wa Faruk afuwa.

Daga bisani, an wanke Faruk daga dukkan zargin da ake masa aka sako shi daga gidan gyaran hali a ranar 25 ga watan Janairun 2021.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaban kamfen ɗin Atiku, Gbenga Daniel, ya fice daga PDP ya koma APC

Cywiński a wani wallafa da ya yi a shafin intanet na Auschwitz-Birkenau Memorial, "ta ce rayuwar Faruq na cikin hatsari saboda barazanar da ya ke samu daga kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi".

Direktan ya ce, "Domin kare yiwuwar kai masa hari, an sauya wa Omar wurin zama nan take bayan sakinsa".

Sai dai direktan bai bayyana sabon inda aka mayar da Faruk ba.

Auschwitz-Birkenau Memorial and Museum ta ce tana shirin taimakawa Faruk, "ya gina sabuwar rayuwa. Hakan zai danganta da kudin da aka samu, muna shirin samar masa sabon gida da a wani wuri da ba Kano ba inda aka zarge shi aka masa shari'a, mu biya masa kudin makaranta sannan mu biya wani kaso na kudaden da lauyoyinsa suka kashe a Nigeria."

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel