Dan Nijar ne ba bahaushe ba ya kashe bayarabe a Shasha, in ji shaidar gani da ido
- Wata mace da ta ce sunan ta Nana Aisha ta bada labarin yadda rikicin kabilanci na kasuwar Sasha a Ibadan ya fara
- Shaidar gani da idon ta ce wani dan Nijar ne ya zubar da tumatur a gaban shagon wata bayarabiya ita kuma ta ce sai ya wanke mata shago
- A yayin da ya ke bata hakuri sai wani bayareba ya tsoma baki a zancen ya kuma mari dan Nijar din sai shima ya rama kuma bayeraben ya fadi kasa ya mutu
Wata shaidar gani da ido ta bada labarin abinda ya faru a kasuwan Shasha da ke Ibadan a jihar Oyo da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 20 da asarar dukiyoyin miliyoyin naira.
A bidiyon da ya bazu a ranar Litinin, wata shaidar gani da ido da ta ce sunanta Nana Aisha ta yi gyara game da ikirarin da aka yi da farko na cewa wani bahaushe ne ya kashe bayarabe inda ta ce wani dan Nijar ne.
KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah
Ta ce rikicin da ya faru tsakanin Hausawa da Yarbawa mazauna garin ya faru ne bayan wani dan Nijar ya zubar da tumatur a gaban shagon wata bayarabiya kuma ta dage sai ya wanke mata shagonta.
A lokacin da mutumin ke bata hakuri kafin ya samo ruwa, wani bayarabe ya tsoma baki a maganan ya kuma shararawa dan Nijar din mari.
Dan Nijar din ya rama marin inda bayaraben ya zame ya fadi a kasa ya kasa tashi. Daga nan yan uwansa suka kai shi asibiti inda likitoci suka tabbatar da ya mutu.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji 18 ciki har da abokan ango a Niger
"Daga nan yan daban Shasha suka fusata suka fara kashe Hausawa. Suna tsammanin da gaske hausawa suka tada rikicin, ba su san cewa Dan Nijar ne ya mari wani har ya mutu ba. Don haka ina shawartar ku da ku rika bincike kafin ku wallafa abinda ba dai-dai bane. Abu daya da za a wallafa zai iya sanadin rikicin kabilanci. Rubutu daya ya janyo an kashe mutane da yawa," a cewarta.
Ta kara da cewa rubutun da wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa na ikirarin cewa bahaushe ne ya kashe bayerabe ya tada rikicin kabilancin da ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi har da kai ga gwamnati ta rufe kasuwar.
Ga bidiyon abinda shaidar gani da idon ta fadi a kasa:
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng