'Yan bindiga sun sace fasinjoji 18 ciki har da abokan ango a Niger

'Yan bindiga sun sace fasinjoji 18 ciki har da abokan ango a Niger

- Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji 18 da suka fito daga Kontagora za su tafi Minna

- Cikin fasinjoji 18 da aka sace, akwai abokan ango da za su tafi daurin aure a Kontagora, jihar Niger

- Gwamnatin jihar Niger ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce za a ceto su tare da tabbatar hakan bai cigaba da faruwa ba

Yan bindiga sun sace fasinjoji 18 a cikin motar hukumar sufuri ta jihar Niger (NSTA), kamar yadda LIB ta ruwaito.

An kai harin ne a hanyar Zungeru-Tegina a kauyen Yakila da karamar hukumar Tafi da ke jihar misalin karfe 3 na ranar Lahadi 14 ga watan Fabrairun 2021.

'Yan bindiga sun sace fasinjoji 18 ciki har da abokan ango a Niger
'Yan bindiga sun sace fasinjoji 18 ciki har da abokan ango a Niger. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun sace amarya da ango a lokacin bikin aurensu

Fasinjoji da aka sace sun hada da wasu abokan ango da ke kan hanyarsu ta zuwa Minna daga Kontagora a yayin da harin ya faru.

Shugaban hukumar bada taimakon gaggawa na jihar Niger, Mallam Ibrahim Inga ya tabbatarwa Daily Trust afkuwar lamarin inda ya ce sun tarar da wata mace da dan ta da yan bindigan suka kyalle.

"Abinda zan iya cewa kawai shine mun ceto matar da danta kuma tana cikin mota tare da mu a hanyar mu na zuwa Minna. Ta fada mana yan bindigan sun tare hanya sun tafi da fasinjoji 18 da ke motar," in ji shi.

KU KARANTA: 'Rabo na da cin abinci tun ranar Juma'a', Ɗan kasuwa ya yi magana kan rikicin Shasa

A bangarenta, gwamnatin jihar Niger ta yi kira ga al'umma su kwantar da hankulansu.

Sanarwar da kwamishinan sadarwa da tsare-tsare na jihar Niger, Hon. Mohammed Sani ya tabbatar da sace mutanen da ke motar ta NSTA da wadanda ake zargin yan bindiga ne suka kai wa hari.

Ya ce gwamnatin jihar ta damu matuka kan lamarin inda yace za ta ceto su ta kuma tabbatar hakan bai cigaba da faruwa ba a jihar.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel