El-Rufa'i: Ba addu'a hukumomin tsaron Nigeria ke bukata ba

El-Rufa'i: Ba addu'a hukumomin tsaron Nigeria ke bukata ba

- An gudanar da taron masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro da tawagar wakilan fadar shugaban kasa

- Taron, wanda aka gudanar a Jihar Kaduna, ya samu halartar gwamnonin Jihohin arewa da sarakunan gargajiya

- Babagana Monguno, mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, shine ya jagoranci tawagar wakilan gwamnatin tarayya

Nasir El-Rufa'i, gwamnan jihar Kaduna, ya ce hukumomin tsaron Nigeria suna bukatar makamai na zamani ba addu'a ba kafin su iya magance ta'addanci da 'yan ta'adda.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayin taro na musamman da aka gudanar tsakanin gwamnonin jihohin arewa da sarakunan gargajiya, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ne ya jagoranci tawagar wakilan gwamnatin tarayya a wurin taron da aka gudanar a Kaduna.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da batun tsaro ya shafi kowa, ya kamata gwamnati ta bashi kulawa ta musamman.

KARANTA: Muhawara: Kalaman Ganduje barazana ce ga rayuwar Sheikh Abduljabar; Lauya Rabiu ya koka

"Akwai masu ruwa da tsaki da dama da basu samu damar halartar wannan taron ba saboda an aika musu gayyata a cikin takaitaccen lokaci.

El-Rufa'i: Ba addu'a hukumomin tsaron Nigeria ke bukata ba
El-Rufa'i: Ba addu'a hukumomin tsaron Nigeria ke bukata ba
Asali: Twitter

"Kullum 'yan bindiga kara samun karfin gwuiwa suke yi, har sojoji suke kai wa hari. Wasu gani ma suke yi tamkar babu wani abu da ake yi akan matsalar tsaro.

"Akwai bukatar mu bawa hukumomin tsaro gudunmawa, amma ta makaman zamani ba ta addu'a ba. Alhakin tabbatar da tsaro ya rataya akan wuyan kowa," a cewar El-Rufa'i.

KARANTA: Miyetti Allah: Tura ta kai bango, zamu dauki fansar mambobinmu da aka kashe

A baya Legit.ng ta rawaito cewa wata tawaga a karkashin mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Babagana Monguno, za ta fara gudanar da wani rangadi domin neman mafita akan matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasa.

A cikin wata sanarwa da Monguno ya fitar ranar Lahadi, ya ce tawagarsa za ta fara ganawa da gwamnonin jihohin arewa ta yamma a garin Kaduna ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu.

A cewarsa, an kirkiro wannan tsari ne na ganawa da shugabannin da masu ruwa da tsaki domin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasa.

Naziru Dalha Taura Malamin makaranta ne kuma dalibi da ke sha'awar rubuce-rubuce akan dukkan al'amuran da suka shafi jiya da yau. Ya samu kusan shekaru hudu yana aiki da Legit.ng.

Ya kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Bayero da ke Jihar Kano a bangaren ilimin kimiyyar sinadaran rayuwa da tasirinsu a jikin dan adam.

Za'a iya tuntubarsa kai tsaye a shafinsa na tuwita a @deluwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel