Miyetti Allah: Tura ta kai bango, zamu mayar da martani akan kisan makiyaya
- Babban kungiyar Fulani Makiyaya, Miyetti Allah, ta ce ta gaji da cin kashi da barazanar da ake yi wa mambobinta
- Rahotanni na cigaba da bayyana yadda ake kara samun yawaitar kai hare-hare akan makiyaya da ke zaune ko xiyartar kudancin Nigeria
- Shugaban kungiyar Miyetti Allah ya ce makiyayan da ake kashewa daban da wadanda suke tafka barna a sassan Nigeria
Saleh Alhassan, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Haure na kasa, ya ce kungiyar a shirye ta ke ta mayar da martani kan kashe mambobin ta da ake yi a fadin Nigeria.
A tattaunawar sa da jaridar The PUNCH, Alhassan ya yi ikirarin cewa da yawan makiyayan da ake kai masu farmaki da kashe su a fadin kasar, mutane ne da basu ji ba basu gani ba.
Ya ce kungiyar ba za ta lamunci cin kashi da barazanar da ake yi wa makiyaya na su fice daga shiyyar Kudu maso Yamma ba.
"Babu wani wanda ya ke da iko (na korar makiyaya). Idan ka ce za ka kori makiyaya, za mu bijirewa wannan umurnin naka. Mun jima muna rayuwa a mawuyacin hali. Idan har ba mu yi bore ba, to karshe za a kakkabe mu daga doron kasa.
KARANTA: Sojoji sun dakile harin kwanton bauna tare da kashe 'yan Boko Haram 19 a Rann
"Idan ka kashe makiyayi, kar ka je ka yi bacci, za mu sake ziyartar ka, kuma ba wai don mun tsani kabilar ka ba ne. Mutane suna kaiwa makiyaya farmaki, kuma a hanyoyi daban daban, makiyaya sun gano yadda za su rinƙa daukar fansa," a cewar Alhassan.
"Duk wadanda su ka tafi zuwa jamhuriyar Benin, yanzu suna dawowa gida. Duk wadanda ke cewa za su haramta bakin makiyaya shigowa Nigeria to basu ma san me suke yi ba, ko ba su karanci dokar ECOWAS ba, babu wanda ya isa ya kore su.
"Wannan ya sa matakin da gwamnan jihar Bauchi ya dauka shine dai dai. Ba ka da wani iko na korar wani mutum daga wani yanki na Nigeria."
KARANTA: Ba a sulhu da ƴan ta'adda: Jayya ta barke tsakanin El-Rufai da Sheikh Gumi martani
Rahotanni sun bayyana cewa ana samun ci gaba da fuskantar matsalar rashin zaman lafiya a shiyyar Kudu maso Yamma, inda ake zargin makiyaya na kai wa mutane farmaki, yayin da a hannu ɗaya, ana ta ganin yadda ake kashe makiyayan a shiyyar ta Kudu.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya karbi bakuncin wata tawagar da ta dauki alhakin yin wa'azi domin shiryar da 'yan bindiga.
A jawabin da ya gabatar yayin karbar tawagar, Tambuwal ya sanar da su cewa matsalar tu'ammali da miyagun kwayoyi na kara rura wutar rashin tsaro.
Tambuwal ya bayar da labarin da wani gwamna ya bashi dangane da abinda ya faru har ya san cewa matan Fulani na safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda.
Naziru Dalha Taura Malamin makaranta ne kuma dalibi da ke sha'awar rubuce-rubuce akan dukkan al'amuran da suka shafi jiya da yau. Ya samu kusan shekaru hudu yana aiki da Legit.ng.
Ya kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Bayero da ke Jihar Kano a bangaren ilimin kimiyyar sinadaran rayuwa da tasirinsu a jikin dan adam.
Za'a iya tuntubarsa kai tsaye a shafinsa na tuwita a @deluwa
Asali: Legit.ng