Muhawara: Kalaman Ganduje barazana ce ga rayuwar Sheikh Abduljabar; Lauya Rabiu ya koka

Muhawara: Kalaman Ganduje barazana ce ga rayuwar Sheikh Abduljabar; Lauya Rabiu ya koka

- Lauyan da ke kare Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara, Barista Rabiu Shuaibu Abdullahi, ya yi korafai akan kalaman Ganduje

- A tattaunawar da aka yi da shi, Barista Rabiu ya yi zargin cewa Ganduje ya bukaci Limaman Kano su tunzura jama'a akan Shekh Kabara

- A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana cewa gwamna Ganduje ya amince a gudanar da muhawara tsakanin Abduljabar da sauran manyan Malaman Kano

Barista Rabiu Shuaibu Abdullahi, Lauyan Malamin addinin Musulunci da ke Kano, Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara, ya yi korafi akan Kalaman gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A cewar Lauyan, kalaman Ganduje suna da hatsari ga zaman lafiya da rayuwar Sheikh Kabara.

A yayin da yake tattaunawa da jaridar Daily Trust, Barista Rabiu, ya bayyana cewa, "mutumin da nake karewa ba ya fuskantar barazana daga wurin kowa sai daga wurin gwamnatin da ya kamata ta bashi kariya.

"Ku je ku saurari maganganun da gwamna ya yi yayin ganawarsa da limaman Jihar Kano a ranar Alhamis din da ta gabata, ya basu umarnin akan abinda da zasu fada yayin hudubar Sallar Juma'a. Ya bukaci su tunzura jama'a akan Abduljabar tare da tura jami'an tsaro su kuma bashi kariya.

KARANTA: Duban kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu

Muhawara: Kalaman Ganduje barazana ce ga rayuwar Sheikh Abduljabar; Lauya Rabiu ya koka
Muhawara: Kalaman Ganduje barazana ce ga rayuwar Sheikh Abduljabar; Lauya Rabiu ya koka
Asali: Twitter

"Idan kai ne zaka yarda da jami'an tsaron? Ta yaya mai sukar lamuranka zai yi ikirarin cewa zai baka kariya. Shi yasa bama ganin barazana daga wani bangare sai daga Kalaman gwamna," a cewarsa.

KARANTA: Ba a sulhu da ƴan ta'adda: Jayayya ta barke tsakanin El-Rufai da Sheikh Gumi martani

Da aka tambaye shi ko yana ganin gwamna Ganduje yana son daukar fansa ne akan Malamin saboda rashin goyon bayansa a zaben 2019, sai ya ce, "me yasa bai dauki mataki akansa a wancan lokacin ba? Me yasa sai yanzu? wannan magana ce ta harkar addini ba siyasa ba.

"Bai kamata ya fake da kungiyar Malaman addini domin daukan fansar abinda ya shafi siyasa ba. Shi shugaba kamata ya yi ace yana da yalwar zuciyar da zai jure abubuwan da na kasa da shi suka yi masa. Dole ne sai ya dauki fansa?" Lauyan ya tambaya.

A makon da ya gabata ne Legit.ng ta rawaito cewa Ganduje ya shirya taron muhawara a tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, da sauran manyan Malamai daga sauran dariku domin a bajeta a faifai.

Kafin hakan, gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwar dakatar da Abduljabar daga gudanar da wa'azi tare da rufe Masallacinsa.

Sai dai, rahotanni sun wallafa cewa a wani yunkuri na warware sabanin fahimta da ke tsakanin Abduljabar da sauran Malaman dariku, gwama Ganduje ya sanar da cewa za'a gudanar da muhawara.

Naziru Dalha Taura Malamin makaranta ne kuma dalibi da ke sha'awar rubuce-rubuce akan dukkan al'amuran da suka shafi jiya da yau. Ya samu kusan shekaru hudu yana aiki da Legit.ng.

Ya kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Bayero da ke Jihar Kano a bangaren ilimin kimiyyar sinadaran rayuwa da tasirinsu a jikin dan adam.

Za'a iya tuntubarsa kai tsaye a shafinsa na tuwita a @deluwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: