Za mu yi ramuwar gayya idan aka hana makiyaya zaman kudu, Kungiyar Fulani
- Sakataren kungiyar samar da cigaban Fulani a Najeriya, a wata tattaunawa da aka yi dashi ya kawo shawarwarin kawo karshen rikicin makiyaya da manoma
- Farfesa Umar Labdo ya ce yadda gwamnan jihar Ondo ya bukaci makiyaya su kwashe ya nasu ya nasu su bar jiharsa rashin kyautawa ne garesu
- A cewarsa, duk da harkokin damfarar yanar gizo da Yarabawa suke yi, Ibo kuma suna sayar da miyagun kwayoyi, babu gwamnan da ya taba fatattakarsu
Farfesa Umar Labdo sakataren kungiyar samar da cigaban Fulani ne wato FULDAN, sannan kuma farfesa ne a bangaren siyasar musulunci a jami'ar Yusuf Maitama Sule dake jihar Kano.
A wata tattaunawa da aka yi da shi ya bayyana tushen rikicin makiyaya da manoman kasar nan da kuma yadda za a shawo kan lamarin.
Kamar yadda yace, "Yadda aka bai wa Fulani kwanaki su tattara kayansu ba a kyauta ba, in dai har ana neman zaman lafiya. Akwai Yarabawa da suke damfara a yanar gizo da Ibo da suke sayar da miyagun kwayoyi a jihata wacce nake zama a arewa. Kuma suna zaune lafiya sana sana'o'insu babu wanda yace su kwashe kayansu.
KU KARANTA: Sojin Najeriya basu son ganin karshen ta'addanci saboda suna amfana da shi, Sheikh Gumi
"Don an san Fulani da garkuwa da mutane baya nufin duk wani bafulatani ne yake haka. Ai ba a yin jam'i. Duk wani bafulatani da aka samu da wannan laifin ai hukunta shi ya kamata a yi ba wai ace ya bar jiha ba."
Ya kara da bayyana yadda Fulani suke da tsagwaron dukiya ta shanu amma sun gwammaci zama a daji, Vanguard ta ruwaito.
Farfesa Labdo yace babu wani bafulatani nagari da zai fatattaki 'yan kudu daga jiharsu, amma idan aka yi musu za su rama.
A cewarsa, "Bafulatani ba zai taba bai wa wani kabila lokacin barin jiharsa ba. Kuma matsawar aka cigaba da hantararsu, za su iya yin bore. Kuma gaba daya kasar za ta iya rudewa a rasa ta inda za a shawo kan lamurran."
"Wajibi ne gwamnati ta tsaya tsayin-daka wurin ganin sun shawo kan wannan rikicin tun kafin al'amarin ya lalace gaba daya," kamar yadda ya tabbatar.
KU KARANTA: Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje
A wani labari na daban, gwamnatin daular Larabawa (UAE) ta dakatar da shigar da 'yan Najeriya zuwa Dubai a matsayin hanyar dakatar da yaduwar cutar COVID-19.
Wannan umarnin ya biyo bayan sa'o'i 24 da da jiragen UAE suka sanar da wannan dakatarwar jirage daga Legas zuwa Abuja.
Babban jirgin da yake kai mutane Dubai daga Najeriya, Air Peace, ya sanar da wannan umarnin na UAE ga fasinjoji.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng