Legas, Kwara, Oyo a kan gaba yayinda mutane 1005 suka kamu da Korona ranar Juma'a
- Adadin masu kamuwa da Korona ya fara sauka a kwanakin nan
- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa
- Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan dokar hukunta masu saba dokokin da NCDC ta kafa
A ranar Juma'a, 12 ga watan Febrairu 2021, Mutane 1,005 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.
Hakazalika an sallami mutane 507 a ranar.
Daga cikin wadanda aka sallama, akwai mutane 408 da sukayi jinya cikin gidajensu a Legas, 99 a Plateau.
Abin takaici, mutane 24 sun rasa rayukansu.
Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 144,521 a Najeriya.
Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 118,866 yayinda 1,734 suka rigamu gidan gaskiya.
KU KARANTA: Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota
KU DUBA: Gwamnan jihar Bauchi mashirmanci ne, dan rikici ne, bai cancanci mulki ba, Gwamnan Ondo
A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan sabon dokan daurin watanni 6 a gidan kaso kan duk wanda aka kama yana saba dokokin kariya daga cutar Korona.
Shugaban kasan ya rattafa hannunsa dokar a Abuja, ranar Laraba.
Kamar yadda dokar killata, sashe 34 na sabon dokan ya tanada, duk wanda ya saba, za'a ci shi tara ko kuma yayi watanni shida a Kurkuku.
Asali: Legit.ng