Da duminsa: Gwamnan jihar Bauchi mashirmanci ne, dan rikici ne, bai cancanci mulki ba, Gwamnan Ondo

Da duminsa: Gwamnan jihar Bauchi mashirmanci ne, dan rikici ne, bai cancanci mulki ba, Gwamnan Ondo

- Gwamnan jihar Ondo ya yiwa Kauran Bauchi wankin babban bargo

- Wannan ya biyo bayan caccakn da gwamnan Benue, Samuel Ortom ya yiwa gwamnan na Bauchi

- Dukkan wanann ya biyo bayan kalaman da gwamna Bala yayi kan rikicin makiyaya

Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akeredolu, ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir, kuma ya siffanta shi matsayin dan rikici da tarzoma.

Akeredolu wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma ya yiwa Bala Kauran wankin babban bargo ne kan maganar da yayi cewa Fulani Makiyaya na da hakkin rike bindigu don kare kansu.

A farkon makon nan gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa Makiyaya na rike bindigogi ne domin kare kawunansu daga masu satar shanu, suna kwashe muku dukiya.

Hira da jaridar Vanguard a Akure, gwamnan Ondo ta bakin kwamishanan labaransa, Donald Ojogo, yayi Alla-wadai irin kalaman da gwamna Bala yayi.

Da duminsa: Gwamnan jihar Bauchi mashirmanci ne, dan rikici ne, bai cancanci mulki ba, Gwamnan Ondo
Da duminsa: Gwamnan jihar Bauchi mashirmanci ne, dan rikici ne, bai cancanci mulki ba, Gwamnan Ondo Credit: Bala Mohammed/Rotimi Akeredolu
Asali: Facebook

KU DUBA: Shugaba Buhari ya nada wani sabon shugaban tsaro

"Idan da gaske ya fadi hakan kuma ya yarda, lallai gwamnan jihar Bauchi yayi magana a madadin gwamnatin tarayya kenan cewa ya halatta dukkan yan Najeriya, har da makiyaya, su rike haramtattun makamai irinsu AK don kare kansu," yace.

"Abinda gwamnan ke kokarin fadi shine ko mu yarda ko kada mu yarda, wajibi ne makiyaya su rike bindiga AK47 don kare kansu amma sauran yan Najeriya su zuba ido tsagerun yan bindiga na kashesu."

"Da wannan kalaman da gwamnan Bauchi yayi, lallai mun shiga cikin wani sabon halin rikici kenan."

"Bai cancanci rike kujeran mulki ba,mutane irinsa masu halaye irin nashi ba su cancanci mulkan jama'a ba."

"Maganar banza yayi, kuma babu inda ya cancanci a jefar da kalaman illa kwandon shara."

DUBA NAN: Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota

A bangare guda, gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana bacin ransa kan takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda ya daura masa laifin halin da Fulani makiyaya ke ciki, rahoton Daily Trust.

Yayin magana a ranar Alhamis, gwamna Bala ya tuhumi Ortom na tsananta rikicin manoma da makyaya ta irin maganganun da yake yi.

Amma mai magana da yawun Ortom, Terver Akase, a martaninsa, ya ce gwamna Ortom ya yi mamakin kalaman gwamna Bala saboda yana kira ga sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da ya rantse zai kare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel