Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota

Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota

- Gwamna Zulum ya sake yiwa wani ma'aikaci babban kyauta bisa kokarinsa

- Wannan karon, wani Likita ne wanda ya kwashe shekaru 6 yana aiki babu albashi

- Gwamnan ya jinjina masa bisa kokarinsa da jajircewansa ga al'ummar Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da biyan kudi N13.9 million da kyautar mota ga Likita dan jihar Ogun, wanda ke ya cigaba da aiki a asibitin Monguno bayan shekaru shida da ritaya.

Gwamnan ya jinjinawa Likitan wanda ya cigaba da aiki babu albashi duk hadarin da ke Munguno sakamakon yakin Boko Haram.

Zulum ya bayyana cewa Dr. Isa Akinbode ya kwashe shekaru 22 yana aiki a jihar Borno kafin yayi ritaya a 2016 a Asibitin Monguno.

Bayan ritayarsa, Likitan da Boko Haram suka taba sacewa a Monguno ya cigaba da aiki kyauta

A baya, tsohon gwamna Kashim Shettima ya kai ziyara Monguno inda ya umurci ma'aikatan ma'aikatar su dauki Dr Akinbode akan kwantaragi.

Amma saboda wasu dalilai, ma'aikatan har yau basu dauki Likitan ba amma duk da haka ya cigaba da aiki.

DUBA NAN: Gwamnan jihar Bauchi mashirmanci ne, dan rikici ne, bai cancanci mulki ba, Gwamnan Ondo

Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota
Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota Credit: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

KU DUBA: Oshiomhole ya soki aikin da shugaban APC ya kirkiro, ya goyi bayan Tinubu, Akande

Bayan shekaru biyar, gwamna Zulum a ranar Juma'a ya bada umurin biyan Likitan kudin albashinsa tun daga lokacin da yayi ritaya a 2016 zuwa yanzu N13.9m.

Hakazalika ya bada umurnin biyan Likitan kudin albashi kowani wata kamar yadda aka shar'anta a kwantiragin.

Daga bisani gwamnan ya bashi kyautar mota Toyota Highlander kan ayyukan da ya yiwa al'ummar jihar Borno.

"Mutane irin (Dr Akinbide) ya kamata a rika karawa karfin gwiwa, yana zaune a Monguno duk da matsalolin tsaro. Magabaci na a ziyarar da ya kawo Monguno ya bada umurnin mayar da shi bakin aiki kan kwantiragi amma wasu dalilai ba'ayi ba," Zulum yace

"Domin cika alkawarin maigidana, na yanke shawaran sake daukansa kwantiragi."

"Zamu biya dukkan bashi albashin da yake binmu, zan bashi kudi N13.9m."

Bayan haka, Zulum ya ce a dauki diyar Likitan aiki a daya daga cikin ma'aikatun jihar Borno.

Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota
Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota Credit: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Samuel Adebayo a matsayin sabon babban hafsan leken asirin tsaro na Najeriya (CDI) kuma shugaban hukumar leken asirin tsaro na kasa(DIA).

Gwamnatin Najeriya ta sanar da nadin sabon kwamandan tsaron a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel