A daure duk wanda ya saba dokar COVID-19 cikin Kurkuku na tsawon wata 6, Buhari

A daure duk wanda ya saba dokar COVID-19 cikin Kurkuku na tsawon wata 6, Buhari

- Najeriya ta kafa sabuwar dokar hukunta masu saba dokokin da aka kafa don dakile yaduwar COVID-19

- A ranar Talata, mutane 15 suka rasa rayukansu sakamakon cutar

- Adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya ta zarce milyan 100

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan sabon dokan daurin watanni 6 a gidan kaso kan duk wanda aka kama yana saba dokokin kariya daga cutar Korona.

Shugaban kasan ya rattafa hannunsa dokar a Abuja, ranar Laraba.

Kamar yadda dokar killata, sashe 34 na sabon dokan ya tanada, duk wanda ya saba, za'a ci shi tara ko kuma yayi watanni shida a Kurkuku.

Me dokar ta kunsa?

"Dokar ta kunshi baiwa juna tazara a dukkan taruka, yayinda dukkan wadanda zasu kasance a wajen su sanya takunkumin rufe fuska, su wanke hannayensu, kuma a duba zafin jikinsu kafin su shiga.

Hakazalika dokar ta tanadi kada a samu mutane sama da 50 a waje guda, illa wuraren Ibada."

KU KARANTA: Hausawa mutanen kirki ne, Fulani ne matsalan Najeriya: Nnamdi Kanu

A daure duk wanda ya saba dokar COVID-19 cikin Kurkuku na tsawon wata 6, Buhari
A daure duk wanda ya saba dokar COVID-19 cikin Kurkuku na tsawon wata 6, Buhari hoto: @NCDCgov
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin gwamnonin Najeriya 11 da suka kamu da cutar Coronavirus

A bangare guda, kasar Sin ta fara yiwa al'ummarta gwajin cutar Korona ta hanyar tura auduga cikin dubura, wannan wata hanya ce da masana sukace tafi bada sakamako na kwarai, Daily Mail ta ruwaito.

Domin yin wannan gwaji, ana bukatar tura audugar cikin dubura na tsawon inci daya zuwa biyu kuma a juyashi.

Bayan yin haka sau biyu, za'a cire audugar sannan ayi gwaji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng