Kotu ta aika mutum 3 gidan yari a kan zargin bai wa 'yan bindiga bayanan sirri

Kotu ta aika mutum 3 gidan yari a kan zargin bai wa 'yan bindiga bayanan sirri

- Wata babbar kotun majistare ta bukaci a adana mata wasu mutum uku a gidan gyaran hali

- Kamar yadda aka gano, suna kai wa 'yan bindiga bayanan sirri wanda ke basu damar satar jama'a

- Dan sanda mai gabatar da kara ya bukaci karin lokaci domin basu damar bincike kan lamarin sosai

Wata babban kotun majistare da ke jihar Katsina ta bukaci a adana mata wasu mutane uku a gidan gyaran hali da ke jihar.

Kamar yadda kotun ta bayyana, ana zargin Aminu Isiya, Lawal Kanjal da Iliya Adam da laifin kai wa 'yan bindiga bayanan sirri, The Punch ta wallafa.

Dukkan mutum ukun 'yan karamar hukumar Kurfi ne da za a adana har zuwa ranar 13 ga watan Afirilun 2021 lokacin da za a kira shari'ar.

KU KARANTA: Kada ku ga laifin makiyaya idan suna yawo da miyagun makamai, Gwamnan Bauchi

Kotu ta aika mutum 3 gidan yari a kan zargin bai wa 'yan bindiga bayanan sirri
Kotu ta aika mutum 3 gidan yari a kan zargin bai wa 'yan bindiga bayanan sirri. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

A ranar Alhamis 'yan sanda sun bayyana yadda aka gurfanar da Isiya bayan kama shi da aka yi a kan zarginsa da ake yi.

Isiya da kan shi ya kira sunan Kanjal da Adam a matsayin wadanda suke taimaka masa wurin aika-aikar.

An gano cewa su ukun suna samarwa 'yan bindiga bayanai wanda suke amfani da shi wurin garkuwa da mutane a yankin. Sune suka bada bayanin da aka yi amfani da shi wurin sace Fiddausi da Fauziya Sani.

An gano cewa an sace 'yan matan biyu daga kauyen Daram da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar.

An gano cewa 'yan bindigan sun kai hari kauyen bayan mutum ukun sun bada bayanan sirri ga wani shugaban 'yan bindiga mai suna Saminu Kwano.

Tuni 'yan sanda suka fara tuhumarsu da hada kai wurin aikata laifi, zama 'yan kungiyar 'yan ta'adda da kuma taimakawa garkuwa da mutane.

Sajan Lawal Bello ya sanar da kotu cewa wadannan laifukan sun ci karo da sashi na 59, 288, 46 da 243 na dokokin Penal Code na Katsina.

Bello ya sanar da kotun cewa ana cigaba da bincike a kan lamarin kuma ya bukaci a dage shari'ar zuwa nan gaba.

Hajiya Fadile Dikko, alkalin kotun ta karba wannan bukatar kuma ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 13 ga watan Afirilun 2021.

KU KARANTA: Da duminsa: UAE ta haramtawa 'yan Najeriya zuwa Dubai saboda Covid-19

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya soki furucin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi akan matsalar rashin tsaron yankin arewa maso yamma, Punch ta wallafa.

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce rashin jajircewar gwamnonin yankin arewa maso gabas ne ya sanya kullum rashin tsaro yake hauhawa a yankin.

Sai dai a wata hira da gidan rediyon faransa (RFI) suka yi da shi a Kano a ranar Alhamis, Ganduje ya ce El-Rufai ba zai taba fahimtar kokarin da gwamnoni suke yi ba na umartar jami'an tsaro.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel