Babu yan majalisan da suka kai mu shan wahala a duniya, Dan majalisar wakilai
- Hanarabul Benjamin Kalu ya bayyana dalilin da ya sa yan majalisa ke yawan mutuwa yanzu
- Dan majalisan ya bayyana cewa yan Najeriya musamman mutan mazabunsu na damunsu da yawa
- Yan bayyana cewa yan majalisan ba sa wani rayuwan jin dadi
Yan majalisai dokokin tarayyan Najeriya ne mafi fama da talauci a duniya, mai magana da yawun majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya bayyana.
Kalu ya bayyana haka ne yayin amsa tambaya kan zargin da ake yiwa wasu yan majalisa na amsan rashawa, The Nation ta ruwaito.
Ya yi watsi da zarge-zargen inda ya ce annobar COVID-19 ce ta janyo musu jinkiri wajen kammala bincike-bincike.
Kalu ya kara da cewa yan majalisa na rashin lafiya ne saboda irin wutan da yan Najeriya kunna musu.
"Kan maganan rashawa, ai da kun gani a jikin yan majalisa. Wannan shine majalisa mafi fama da talauci. Ba za ku ga yan majalisa na rayuwan jin dadi ba. Wani kudi zasu sata? Wahala kawai muke sha," Kalu yace.
"Dalilin da yasa yawancin yan majalisan dake mutuwa ciwon zuciya ke kashe su. Wahalan da mutanen mazabunsu ke basu yayi yawa."
"Maganar gaskiya itace, ko ku fahimta ko ku ki. Wahalan da mutanenmu ke bamu yake kashe yan majalisar dokokin tarayya. Wannan shine gaskiya. Wahalan yayi yawa," ya kara
Daga 2019 zuwa yanzu, Sanatoci 4 da yan majalisar wakilai 3 suka mutu.
A 2020, N125 billion aka baiwa yan majalisan yayinda suka samu N134 billion a kasafin kudin 2021.
DUBA NAN: Sauya sheka: Kungiyar matasa tana maraba da Fani-Kayode zuwa APC
DUBA NAN: A rana guda, yan bindiga sun kashe mutane 23 a jihar Kaduna
Kun ji cewa, Dan majalisar tarayyar Nigeria mai wakiltar jihar Abia, Ossy Prestige ya riga mu gidan gaskiya.
Dan majalisar mai wakiltar, Aba North/South na jihar Abia ya rasu ne bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng