Sauya sheka: Kungiyar matasa tana maraba da Fani-Kayode zuwa APC

Sauya sheka: Kungiyar matasa tana maraba da Fani-Kayode zuwa APC

- Kungiyar GYB2PYB Youth Support Group ta marabci Fani-Kayode zuwa jam'iyyar APC

- Kungiyar ta bayyana zuwansa jam'iyyar alheri ne wajen sauya Najeriya ba jam'iyyar kadai ba

- Kungiyar ta kuma bayyana cewa zuwansa ya kara wa jam'iyyar girma ba a Najeriya kadai ba

GYB2PYB Youth Support Group ta yabawa Gwamna Yahaya Bello bisa matakan da suka dauka har zuwa yanzu don sanya APC a matsayin babbar jam’iyyar siyasa a Afirka, Vanguard News ta ruwaito.

A jiya gwamnan jihar Kogi tare da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Buni na jihar Yobe sun karbi tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

KU KARANTA: Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC kan zaben 2023 mai zuwa

Sauya sheka: Kungiyar matasa tana maraba da Fani-Kayode zuwa APC
Sauya sheka: Kungiyar matasa tana maraba da Fani-Kayode zuwa APC Hoto: The News Guru
Asali: UGC

Da yake maida martani, GYB2PYB a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Darakta Janar dinta a ranar Talata, Amb. Oladele John Nihi ya ce sauya sheka da ake zargin Fani-Kayode ya yi zuwa APC shawara ce mai kyau ga jam'iyyar, ya kara da cewa

"burin cimma sabuwar Najeriya wani aiki ne na gama gari".

Kungiyar ta ce zargin ficewar da jigon na PDP ya yi zai kawo babban canji ga ci gaban siyasar Najeriya, ta kara da cewa wannan yunkuri da tsohon Ministan ya yi

“ba wai kawai kari bane ba, amma ya nuna karara na nuna gaskiyar jajircewar shugabannin jam’iyyar cewa APC gida ne ga kowa ”.

KU KARANTA: Cin hanci da rashawa na hau-hawa ne saboda ba a daure masu laifi, in ji Amaechi

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta kashe jimillar Naira biliyan 37 a kan shirin tallafawa 'yan Najeriya da aka fi sani da Survival Fund, in ji Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, Nigeria Tribune ta ruwaito.

Kudin, kamar yadda ya sanar, an kashe su ne kan wasu tsare-tsare kamar N50,000 ga masu aiki a ma'aikatu na tsawon watanni uku zuwa sama da aka rabawa mutane 300,000.

An kuma tallafawa wasu masu sana'ar hannu da N30,000 kusan mutum 100,000, da rajistar sunan kasuwanci a CAC na mutane 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta biya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: