A rana guda, yan bindiga sun kashe mutane 23 a jihar Kaduna

A rana guda, yan bindiga sun kashe mutane 23 a jihar Kaduna

- Matsalar tsaro na cigaba da kwasan rayukan mutane a jihar Kaduna

- A rana guda, gwamnatin jihar tayi alhinin kisan mutane sama da 20

- Gwamna El-Rufa'i ya bayyana cewa babu sulhu tsakaninsa da yan bindiga

Gwamnatin jihar Kaduna ta bada rahoton kisan mutan jihar 23 da yan bindiga sukayi a kananan hukumomi biyar na jihar a rana guda kacal.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.

A cewar Aruwan, yan bindigan sun kai wadannan hare-hare ne a iyakokin jihar da wasu jihohin dake makwabta.

Jawabinsa yace: "Sakamakon matsalar tsaron da jihar ke fama da shi cikin sa'o'i 24 da suka gabata, gwamnatin jihar Kaduna ta samu labari daga hukumomin tsaro cewa an kashe mutane 23 a hare-haren da aka kai kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da Kauru."

Aruwan yace mutum 10 aka kashe a karamar hukumar Birnin Gwari kadai.

Sune: Abdu Hasan; Sufyanu Musa; Faisal Zubairu; Abdullahi Hasan; Ali Abdu; Rabiu Aliyu; Zubairu Yau; Bukar Yusuf; Mamman Ibrahim da Dankande Musa.

Wadanda suka jigawa kuwa sune Baushi Alu, Rabe Sani da Usama Sani.

A karamar hukumar Igabi kuwa, Aruwa ya ce yan bindigan sun bindige Dayyabu Yahuza.

A karamar hukumar Giwa, Aruwan yace "yan bindiga sun kai hari kauyen Janbaba, inda suka kashe wani Yakubu Sule,".

DUBA NAN: Babu yan majalisan da suka kai mu shan wahala a duniya, Dan majalisar wakilai

A rana guda, yan bindiga sun kashe mutane 23 a jihar Kaduna
A rana guda, yan bindiga sun kashe mutane 23 a jihar Kaduna Credit: @GovKaduna
Asali: Twitter

DUBA NAN: Sauya sheka: Kungiyar matasa tana maraba da Fani-Kayode zuwa APC

A karamar hukumar Kauru kuwa, Aruwa ya ce mutum biyar aka kashe wanda suka hada da Danlami Sunday; Abbas Abou; Sati Yakubu; Shaba John da John Francis a kauyen Kishisho.

A karamar hukumar Chikun, Aruwan ya bayyana cewa an kashe Habila Ibrahim; Samaila Audu; John Musa; Birnin Aboki da Ali Aboki, a kauyen Gwagwada-Kasaya, yayinda aka kashe Bitrus Joseph a kauyen Agwa.

Aruwan ya kara da cewa an kashe dan bindiga daya, lokacin da mutan garin suka taso musu.

Gwamnan jihar Kaduna, a jawabin, ya yi alhinin wannan hare-hare, yayinda yake jajantawa wadanda sukayi rashi kuma yake addu'a ga wadanda suka jigata.

A bangare guda, babban kwamandan yan bindiga a Zamfara mai suna Auwalu Daudawa ya ce ya amince ya mika bindigunsa ne bayan ya gano kai hare-hare babu riba kuma bata da amfani, Daily trust ta ruwaito.

Daudawa na daya daga cikin wadanda ke jagorantar yan bindiga da ke dajin Dumburum a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Yan kungiyarsa sun dade suna kai hare-hare a hanyar Zurmi - Gidan Jaja da Jibia.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel