Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa dan majalisar Nigeria, Ossy Prestige, rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa dan majalisar Nigeria, Ossy Prestige, rasuwa

- Dan majalisar wakilai na tarayya, Mista Ossy Prestige ya riga mu gidan gaskiya

- Dan majalisar mai wakiltar mazabar Aba North/South daga jihar Abia

- Ya rasu ne bayan ya dade yana fama da rashin lafiya kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta tabbatar

Dan majalisar tarayyar Nigeria mai wakiltar jihar Abia, Ossy Prestige ya riga mu gidan gaskiya, Premium Times ta ruwaito.

Dan majalisar mai wakiltar, Aba North/South na jihar Abia ya rasu ne bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa dan majalisar Nigeria, Ossy Prestige, rasuwa
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa dan majalisar Nigeria, Ossy Prestige, rasuwa. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

An zabe shi ne a karkashin jam'iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA).

DUBA WANNAN: Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa

Mai magana da yawunsa, Benjamin Kalu, shima ya tabbatar ta rasuwar dan majalisar cikin sakon kar ta kwana daya aike wa majiyar Legit.ng.

"Wani daga cikin iyalansa ya tabbatar da rasuwarsa," in ji shi.

Wara majiyar, daga shugabannin majalisar wakilai na tarayya ita ma ta tabbatar da rasuwarsa.

"Eh, da gaske ne ya rasu. Za a sanar yayin zaman majalisar gobe sannan a tashi daga zaman," in ji dan majalisar da ya nemi a sakaya sunansa domin ba a bashi izinin magana kan batun ba.

Marigayi Mista Prestige shine dan majalisar wakilai na tarayya na uku da ya rasu a majalisa zubi ta tara.

Sauran biyun da suka rasu kafin shi sune Ja'afaru Iliyasu da Mohammed Faggen-Gawo.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164