Ya kamata a rika fitar da Zakkah domin shirya fina-finai, daidai yake da gina Masallatai, Aliyu Momo

Ya kamata a rika fitar da Zakkah domin shirya fina-finai, daidai yake da gina Masallatai, Aliyu Momo

- Jama'a a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun tofa albarkatun bakinsu kan maganar shahrarren dan wasan kwaikwayo, Ali Momo

- Momo babban jarimi a masana'antar Kannywood din ya bada fatawar da ba'a taba ji bakin Malamai ba

- Dan wasan kwaikwayon ya bayyana muhimmancin shirya fina-finan Hausa ga addini

Aliyu Momoh ya bayyana ra'ayinsa kan muhimmancin harkar Fim a cikin al'umma inda yayi kira da zuba kudin Zakkah wajen shirya fina-finan Kannywood domin fadakar da mutane.

A ra'ayinsa, ya cancanta a sanya Kannywood cikin tsarin masu karban Zakkah saboda daidai yake da gina Masallatai da Islamiyoyi.

Yace: "Kai Zakkah ma da ake fitarwa, ya cancanta ma a rika fitar da kudade daga cikin tsarin Zakkah wadanda za'a rika shirya fina-finai da fadakarwa da shirye-shirye domin jama'a su amfana."

"Daidai yake da gina Masallatai da Islamiyyu, gwara ka bada kudin ayi shirye-shirye wadanda mutane zasu darasi su amfana saboda tasirinsu."

"Kuma ladan mutum sadakatul jariya ce, duk inda mutum yaje har bayan rayuwarsa."

KU KARANTA: Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota

Ya kamata a rika fitar da Zakkah domin shirya fina-finai, daidai yake da gina Masallatai, Aliyu Momo
Ya kamata a rika fitar da Zakkah domin shirya fina-finai, daidai yake da gina Masallatai, Aliyu Momo
Source: UGC

KU DUBA: Gwamnan jihar Bauchi mashirmanci ne, dan rikici ne, bai cancanci mulki ba, Gwamnan Ondo

A wani labarin kuwa, manyan jarumai mata na Kannywood na can a kasar Dubai suna yawon bude ido da shakatawa. Wannan ya zama kamar al’ada ga wasu yan masana’antar inda suke tafiya chan a duk karshen shekara domin hutawa.

Daga cikin manyan jaruman masana’antar da ke can Dubai akwai Fati Washa, Hafsat Idris, Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi da kuma Maryam Wazeeri.

Jaruman dai kan dora hotunansu a shafukansu na sada zumunta kan tafiyar tasu tare da fadin ‘On Dubai’.

Source: Legit.ng

Online view pixel