Rashida Mai Sa’a tayi zazzafan raddi ga yan matan Kannywood kan zuwa yawon bude ido a Dubai

Rashida Mai Sa’a tayi zazzafan raddi ga yan matan Kannywood kan zuwa yawon bude ido a Dubai

- Tsohuwar jarumar Kannywood, Rashida Mai Sa'a tayi martani mai zafi a kan masu zuwa yawon shakatawa kasar Dubai sannan suke wallafa hotunansu

- Rashida ta bayyana hakan a matsayin kauyanci da rashin sanin ciwon kai inda tace ita kasuwar Rimi ya ma fiye mata zuwa Dubai din

- Manyan jaruman masana'antar Kannywood irin su Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Fati Washa da sauransu na can a kasar Dubai suna shakatawa

Kamar yadda ake ciki a yanzu, manyan jarumai mata na Kannywood na can a kasar Dubai suna yawon bude ido da shakatawa. Wannan ya zama kamar al’ada ga wasu yan masana’antar inda suke tafiya chan a duk karshen shekara domin hutawa.

Daga cikin manyan jaruman masana’antar da ke can Dubai akwai Fati Washa, Hafsat Idris, Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi da kuma Maryam Wazeeri.

Jaruman dai kan dora hotunansu a shafukansu na sada zumunta kan tafiyar tasu tare da fadin ‘On Dubai’.

Rashida Mai Sa’a tayi zazzafan raddi ga yan matan Kannywood kan zuwa yawon bude ido a Dubai
Rashida Mai Sa’a tayi zazzafan raddi ga yan matan Kannywood kan zuwa yawon bude ido a Dubai Hoto: Arewablog
Asali: UGC

Sai dai hakan bai yi wa tsohuwar jarumar masana’antar, Rashida Mai Sa’a dadi ba kan yadda suke yawan nuna ma duniya cewa sunje Dubai din.

KU KARANTA KUMA: Mai laifi ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa

Hakan ne ya sa Rashida ta fitar da wani bidiyo inda tayi suka mai zafi ga matan da suke zuwa can suna damun mutane da cewa sun tafi Dubai.

Duk da dai bata kira sunan wadanda take ma caccakar ba amma dai jama’a suna ganin da jaruman kannywood din da suke can take.

Ta ce: "Gaskiya yan matanmu da zawarawanmu suna ban mamaki, wai ka tafi Dubai kamar wanda ya tafi Aljannah, toh ki tafi Landan mana ko ki je Amurka, ko jamini ko faransa, amma sai a ta wani sa On-Dibai, On-Dibai, kina da yar dubunki 550 sai ki tarkata ki tafi Dibai amma mu kun dame mu dan Allah kauyanci.

"Wai Dibai dinnan kasuwar Rimi ma ta fi mun wahalar zuwa, amma an bi an damemu, shiyasa nace ba zan je Dibai a wannan sabgarba nace a bari yan kauye su je su gama kauyencinsu suna dorawa a status, wai dan ka je Dibai sai ka ta sawa a Instagram kana damun mutane."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Za mu kawo karshen yaki da ta'addanci a wannan shekarar, Buhari ya kaddamar

Ga bidiyon a kasa:

A wani laari na daban, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan, ta cika da farin ciki a yau Juma’a, 8 ga watan Janairu, kasancewarsa ranar zagayowar haihuwar masoyinta, Muhammad Turad Sha'aban.

Hanan wacce a kwanaki ne aka daura aurenta da muradin ran nata, ta wallafa rubutu a shafinta na Instagram inda ta yi wa mijin nata fatan alheri.

Baya ga zantukar soyayya, Hanan ta kuma wallafa wani hotonta da mijinta inda ta sumbace shi a goshinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel