ASP: Buhari ya bullo da sabon tsarin ilimi don 'ya'yan talakawa

ASP: Buhari ya bullo da sabon tsarin ilimi don 'ya'yan talakawa

- Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sanar da bullo da sabon shirin ASP (Alternate School Programme)

- ASP sabon shirin gwamnatin Buhari ne da zai tabbatar da bayar da ilimi kyauta ga yara marasa galihu da basa zuwa makaranta

- Shugaba Buhari ya bayyana cewa burin gwamnatinsa shine bayar da ilimi ga dukkan yaran da ke Nigeria

Shugaban kasa, Muhamadu Buhari, a ranar Laraba ya kaddamar da sabon shirin bayar da ilimi kyauta ga yara marasa galihu da basa halartar makarantu a matakin farko.

Buhari ne da kansa ya sanar da bullo da sabon shirin a cikin wani takaitaccen sako da ya fitar a shafinsa na sada zumunta (Tuwita).

"Mun fara aiki akan sabon shiri na musamman mai taken ASP (Alternate School Programme) domin bayar da ilimi ga yaran da basa zuwa makaranta a fadin kasar nan. Dole ne, kuma nauyi ne da ya rataya a wuyanmu, mu tabbatar da cewa duk yaran da ke Nigeria sun halarci makaranta a matakan farko.

KARANTA: Obasanjo: Akwai banbanci a tsakanin Buharin yanzu da wanda na sani a baya

KARANTA: An kama matasan da ke dillancin hotuna da bidiyon tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo

ASP: Buhari ya bullo da sabon tsarin ilimi don 'ya'yan talakawa
ASP: Buhari ya bullo da sabon tsarin ilimi don 'ya'yan talakawa
Asali: Twitter

"A farkon kaddamar da shirin ASP, za'a fara da koyar da yara darussa a Lissafi, Turanci, Kimiyya a matakin farko (Basic Science) da ilimin zamantakewa (Sociology). Daga bisani za'a gabatar da wasu darussa da zasu taimakawa yaran wajen samun dabaru akan sana'o'i da dabarun dogaro da kai," a cewar shugaba Buhari.

A baya bayan nan ne Legit.ng ta rawaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan dokar kariya daga cutar coronavirus da ke tilasta amfani da takunkumin fuska.

Dokar ta tanadi tara ko daurin wata shida ko gaba daya biyun ga duk wanda ya karya dokar.

Amma a karshen mako, an ga shugaban kasar yana tattaunawa da wasu gwamnonin APC a wajen sabunta rajistar sa ta jam'iyyar APC a Daura ba tare da sanya tukunkumin ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel