FG zata maye gurbin matsayin BVN da NIN bayan CBN ya gamsu da hujjar Pantami
- Ministan sadarwa Dakta Isa Ali Pantami, ya sanar da cewa gwamnatin tarayya tana kan shirin maye gurbin BVN da NIN
- Dakta Pantami ya sanar da cewa ya bayar da gamsassun hujjoji da CBN ta amince da su domin yin sauyin
- A cewar Pantami, NIN ta zama doka a tsarin kundin mulkin Nigeria a yayin da BVN tsarin banki ne kawai
Dakta Isa Ali Pantami, ministan sadarwa da sabon tsarin gina tattalin arziki, ya ce gwamnatin tarayya tana kan hanyar maye gurbin matsayin BVN da NIN.
BVN lamabobi ne na tantancewa da bankuna suke bawa kwastomominsu.
Tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Sanusi Lamido, ne ya bullo da tsarin BVN domin tsaftace harkokin bankuna da kuma magance badakala da cin hanci.
Hukumar bayar da katin shaidar zama dan kasa, NIMC, ce ke bayar da lambobin tantancewa na NIN ga kowanne dan kasa da ya yi rijista da gwamnati.
KARANTA: Fahimta Fuska: Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano
Da yake jawabi ranar Litinin yayin da ya kai ziyara domin ganin aikin rijistar dan kasa a Abuja, Pantami ya ce za'a koma aiki da NIN a bankuna, sabanin amfani da BVN, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
"Tuni na ja hankalin majalisar koli ta bunkasa tattalin arzikin kasa da gwamnan babban bankin kasa (CBN) akan bukatar yin hakan.
"Na bashi hujjar cewa NIN ta fi BVN muhimmanci saboda ita ta kasa ce ba wani bangare daya kadai ba.
"An riga an kirkiri doka akan NIN, ita kuwa BVN tsarin banki ne kawai, wanda bashi da tasiri ko karfi fiye da dokar kasa," a cewarsa.
KARANTA: Kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu
Pantami ya kara da cewa komawa amfani da NIN zai tabbatar da samun karuwar tsaro da tsare sirrin bayanan 'yan kasa.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya karbi bakuncin wata tawagar da ta dauki alhakin yin wa'azi domin shiryar da 'yan bindiga.
A jawabin da ya gabatar yayin karbar tawagar, Tambuwal ya sanar da su cewa matsalar tu'ammali da miyagun kwayoyi na kara rura wutar rashin tsaro.
Tambuwal ya bayar da labarin da wani gwamna ya bashi dangane da abinda ya faru har ya san cewa matan Fulani na safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng