Fani-Kayode na jagoranci, wasu gwamnonin PDP 4 za su sauya sheka zuwa APC

Fani-Kayode na jagoranci, wasu gwamnonin PDP 4 za su sauya sheka zuwa APC

- Yayin da zaben 2023 yake kara matsowa, shugabannin jam'iyyar APC sun fara tattaunawa da wasu gwamnonin PDP 4 kan canja sheka

- A ranar Litinin ne tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya je har Abuja don tattaunawa da Mai Mala Buni da Gwamna Yahaya Bello

- Wani ginshiki na jam'iyyar APC ya bayyana cewa akwai gwamnonin PDP 4 da suke shirin komawa APC, hakan ne yasa mutane suke ganin nasara tana hararar APC

Yayin da kowanne dan siyasa yake shiri akan zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar APC ba a barta a baya ba, sai dai alamun nasara suna ta harararta don yanzu haka gwamnoni 4 na jam'iyyar PDP sun shirya tsaf akan sauya shekarsu zuwa APC.

A ranar Litinin ne aka samu labarin yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya lallaba har babban birnin tarayya, Abuja don tattaunawa da shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Wani mai fadi a ji na jam'iyyar APC ya sanar da Punch cewa gaskiya ne batun zuwan Fani-Kayode wurin shugabannin jam'iyya, duk da dai tsohon ministan bai riga ya fadi wata magana ba tukunna.

Fani-Kayode na jagoranci, wasu gwamnonin PDP 4 za su sauya sheka zuwa APC
Fani-Kayode na jagoranci, wasu gwamnonin PDP 4 za su sauya sheka zuwa APC. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Alaka da 'yan bindiga: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban karamar hukuma a Katsina

Majiyar ta tabbatar da yadda haduwarsu ta haifar da da mai ido.

Kamar yadda yace, "Fani-Kayode ya samu Yahaya Bello da Buni a Abuja a ranar Lahadi, sun tattauna na tsawon sa'o'i 2 akan siyasar 2023 da kuma yadda APC take gudanar da rijistar 'yan jam'iyya."

Da aka tambaye shi akan gwamnonin PDP 4 da suke shirin sauya sheka, cewa yayi ba zai bayyana ba saboda hakan ya zama rashin wayau.

Kamar yadda yace, "Gwamnonin guda 4 suna so su samu tabbacin cewa idan sun canja jam'iyya za a iya basu damar tsayawa takara a jihohinsu. Wannan ne dalilin da ya sanya aketa tattaunawa dasu."

KU KARANTA: Son komawa wasa Turai domin gogayya da manyan 'zakaru' yasa na bar Al Nassr, Ahmed Musa

"Akwai masu shirye-shiryen barin APC don neman wasu mukamai. Za a cigaba da ganin irin haka ai har 2023."

A wani labari na daban, Auwalun Daudawa, wanda ake zargi da shirya sace yaran makarantar sakandaren Kankara da ke jihar Katsina ya tuba.

Daudawa tare da manyan yaransa biyar sun mika bindigogi kirar AK 47 guda 20 da wasu makamai hannun gwamnati, The Cable ta wallafa.

A watan Disamban shekarar da ta gabata, sama da dalibai 300 aka sace daga makarantar kwana a garin Kankara. An samu karbo daliban bayan sun kwashe mako guda a hannun wadanda suka sace su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel