Alaka da 'yan bindiga: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban karamar hukuma a Katsina

Alaka da 'yan bindiga: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban karamar hukuma a Katsina

- 'Yan sandan jihar Katsina sun tabbatar da kama tsohon shugaban karamar hukumar Jibia a kan alakar sirri da 'yan bindiga

- An kama Haruna Musa Mota tare da gurfanar da shi a gaban wata kotu bayan an samu sautin hirarsa da wadanda suka sace daliban Kankara

- A halin yanzu an adana Mota a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a kammala bincike da kuma shari'ar baki daya

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta damke tsohon shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Jibia da ke jihar, Haruna Musa Mota akan zarginsa da alaka da 'yan bindiga.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da kama tsohon shugaban karamar hukumar, Punch ta wallafa.

Ya kara da cewa an kama Mota ne sakamakon zarginsa da ake da taimakawa ayyukan 'yan bindiga a jihar kuma an mika shi a gaban kotu.

KU KARANTA: Karamar yarinyar da ta damki hannun Osinbajo a tsakar kasuwar Nyanya ta zama 'diyarsa'

Alaka da 'yan bindiga: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban karamar hukuma a Katsina
Alaka da 'yan bindiga: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban karamar hukuma a Katsina. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Duk da kakakin rundunar bai sanar da lokacin da aka cafke Mota ba kuma aka gurfanar da shi, wasu majiyoyi sun ce an gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun majistare ne a ranar Juma'a.

An adana shi a gidan gyaran hali na jihar Katsina har zuwa lokacin da 'yan sanda za su kammala bincike kuma ma'aikatar shari'a ta bada shawara a kan shari'ar.

An gano cewa kamen Mota da gurfanar da shi basu rasa alaka da wani sautin murya da aka samu wanda aka ji shi yana waya da 'yan bindiga a watan Disamba a kan satar yaran makarantar Kankara da aka yi.

Duk da an sako daliban, har a halin yanzu ana bincike tare da son gano sarakakiyar dake tattare da satan nasu.

KU KARANTA: Miloniyoyin Najeriya 5 masu karancin shekaru a 2021 da yadda suka tara dukiyarsu

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta zargi jam'iyyar PDP da yin ayyuka masu kama da na Boko Haram. A wata takarda da hadimin Buhari na musamman akan yada labarai, Garba Shehu, ya saki, fadar shugaban kasa ta caccaki jam'iyyar PDP saboda kin amincewa da nadin tsofaffin hafsoshin sojin Najeriya mukami.

Kola Ologbondigan, sakataren PDP na kasa, ya bayyana nada tsofaffin hafsoshin sojin Najeriya a matsayin jakadun Najeriya a kasashen ketare a matsayin abinda bai dace ba, kuma ya bukaci kada 'yan majalisar dattawa ta amince da hakan.

Sai dai Shehu ya ce an nada su ne saboda jajircewarsu da dagewarsu akan Najeriya, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng