Hotunan Auwalun Daudawa tare da mukarrabansu suna mika makamansu tare da tuba

Hotunan Auwalun Daudawa tare da mukarrabansu suna mika makamansu tare da tuba

- Gagarumin dan bindigan da ya shirya satar yaran makarantar Kankara, Auwalun Daudawa ya tuba

- A ranar Litinin ya mika makamansa tare da yaransa biyar kuma suka dauka rantsuwar tuba a Gusau

- Ya bayyana cewa baya bukatar tallafi daga kowa kuma ya tuba ne bayan ya gane gwamnati bata da burin cutar da shi

Auwalun Daudawa, wanda ake zargi da shirya sace yaran makarantar sakandaren Kankara da ke jihar Katsina ya tuba.

Daudawa tare da manyan yaransa biyar sun mika bindigogi kirar AK 47 guda 20 da wasu makamai hannun gwamnati, The Cable ta wallafa.

A watan Disamban shekarar da ta gabata, sama da dalibai 300 aka sace daga makarantar kwana a garin Kankara. An samu karbo daliban bayan sun kwashe mako guda a hannun wadanda suka sace su.

KU KARANTA: Alaka da 'yan bindiga: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban karamar hukuma a Katsina

Hotunan shugaban 'yan bindiga tare da tawagarsa suna mika makamansu ga Matawalle
Hotunan shugaban 'yan bindiga tare da tawagarsa suna mika makamansu ga Matawalle. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya ce kungiyar Miyetti Allah ce ta karbo yaran kuma babu kudin da aka biya na fansa.

A yayin jawabi bayan ya dauka rantsuwar tuba aranar Litinin a gidan gwamnati a Gusau, dan bindigan ya ce tawagarsa sun mika makamansu kuma basu son kudi daga hannun kowa ko kuma gwamnati.

Hotunan shugaban 'yan bindiga tare da tawagarsa suna mika makamansu ga Matawalle
Hotunan shugaban 'yan bindiga tare da tawagarsa suna mika makamansu ga Matawalle. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwamandojin ISWAP Sulum da Borzogo sun sha da kyar, soji sun kwace sansaninsu a Timbuktu

Hotunan shugaban 'yan bindiga tare da tawagarsa suna mika makamansu ga Matawalle
Hotunan shugaban 'yan bindiga tare da tawagarsa suna mika makamansu ga Matawalle. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

"Da kanmu muka tuba kuma bamu bukatar ko kobo daga gwamnati, kungiya ko wani mutum," yace.

"Na sakankance cewa gwamnati na son sasanci da 'yan bindiga. Daga wurin wadanda suka tuba muka ji cewa babu wani shiri da gwamnati take yi na cutar da mu. Mun dawo rayuwa kamar kowanne dan Najeriya mai son zaman lafiya."

Hotunan shugaban 'yan bindiga tare da tawagarsa suna mika makamansu ga Matawalle
Hotunan shugaban 'yan bindiga tare da tawagarsa suna mika makamansu ga Matawalle. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

A bangarensa, Matawalle ya ce wannan cigaban ya samu ne saboda tsabar kokarin gwamnatinsa na ganin Zamfara ta kasance cikin zaman lafiya.

"anan cigaban ba zai saka Zamfara cikin jihohi masu zaman lafiya kadai ba a kasar nan, zai tabbatar da cewa kasuwancinta da ya dade da tabarbarewa zai dawo," Gwamnan yace.

A wani labari na daban, kotun jihar Legas ta laifuka na musamman dake Ikeja ta yanke wa faston Living Faith Church wacce aka fi sani da Winner's Chapel, Afolabi Samuel, shekaru 3 a gidan gyaran hali bisa satar $90,000 da N4,500,000 wanda 'yan coci suka hada karfi da karfe suka tara.

EFCC ta gabatar da Samuel wanda shine akawu kuma ma'ajin cocin gaban alkali Mojisola Dada bisa laifuka biyu, almundahana da sata.

Kamar yadda EFCC ta gabatar, faston da wata Blessing Kolawole, wacce take aiki a jami'ar Covenant, sun hada kulle-kullen satar dukiyar kuma sun sake a aljihunansu don amfaninsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel