Son komawa wasa Turai domin gogayya da manyan 'zakaru' yasa na bar Al Nassr, Ahmed Musa

Son komawa wasa Turai domin gogayya da manyan 'zakaru' yasa na bar Al Nassr, Ahmed Musa

- Sanannen dan wasan kwallon kafa kuma kaftin na Super Eagles, Ahmed Musa ya ce bashi da buri da ya wuce komawa Turai wasa

- Ya sanar da hakan ne bayan barin kungiyar Al Nasssr ta kasar Saudi Arabia da yayi a shekarar da ta gabata

- A cewarsa, babban burinsa shine gogayya da manyan 'yan wasan kwallon kafa na duniya wanda babu dadewa zai fara

Fitaccen dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa mai shekaru 28 yana da dukiyar da ta kai $20 miliyan wanda ya samesu ta hanyar wasan kwallon kafa da tallace-tallace.

A yayin bayani a kan yadda babu zato balle tsammani ya bar kungiyar Al Nasssr da ke Saudi duk da tarihi mai kyau da ya kafa, Musa ya ce yana son komawa manyan gasa ne a Turai.

KU KARANTA: Ba za a iya jan ra'ayinmu don tabbatar da nadin da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaro ba, Majalisa

Ahmed Musa ya sanar da dalilinsa na barin kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia
Ahmed Musa ya sanar da dalilinsa na barin kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Da kan shi ya bukaci ya bar kungiyar kwallon kafan ta Riyadh duk da kuwa shekaru biyu ya kwashe daga cikin kwagilar shekaru hudu da yasa hannu.

Ya sanar da ESPN cewa da kanshi ya mika bukatar barin kungiyar kuma yayi sa'a suka amince.

"Na samu ganawa da kungiyar inda nace ina son datse kwangilata kuma suka yadda," Musa ya sanar da ESPN.

Musa, daya daga cikin 'yan kwallon kafa da aka fi biya a kasar Saudi Arabia, ya ce ya kasance mai burin komawa Turai.

"Na ji dadin zaman shekaru biyu da nayi a can kuma kungiyar kwallon kafan ta kyautata min," Musa ya sanar da ESPN.

"Amma kuma ina son komawa Turai kuma ina tunanin wannan ne lokacin da ya dace in yi hakan.

“Ina son gogayya da manyan 'yan wasan duniya. Ina mika godiyata ga kungiyar Al Nassr da kuma masoyana kan fahimtata da kuma fatan alheri da suke min. Ba zan manta da su ba."

KU KARANTA: Karamar yarinyar da ta damki hannun Osinbajo a tsakar kasuwar Nyanya ta zama 'diyarsa'

A wani labari na daban, sabbin dalilai sun bayyana a kan abinda yasa jigon jam'iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu da kuma uban jam'iyya, Bisi Akande da wasu suke sukar sabunta rijistar da 'yan jam'iyyar ke yi a kasar nan.

Fiye da dalilan da shugabannin biyu suka sanar, majiyoyi da suke tattare da su sun ce zargin wani mugun abu zai bullo daga shugabannin jam'iyyar na yanzu sune sahihan dalilan da suka sa Akande da Tinubu suke sukar rijistar.

Kwamitin rikon kwarya da tsari na jam'iyyar karkashin shugabancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya fara rijistar 'yan jam'iyyar a fadin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel