'Yan bindiga sun tare motar ɗaukan gawa, sun yi awon gaba da ƙanin mamacin

'Yan bindiga sun tare motar ɗaukan gawa, sun yi awon gaba da ƙanin mamacin

- 'Yan bindiga sun tare motar daukar gawa sun sace kanin marigayin da ake dauke da gawarsa

- Yan bindigan sun kuma kashe wani direban mota da ke biye da motar daukar gawar

- Masu garkuwa da mutanen sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan biyar

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a ranar Asabar 6 ga watan Fabrairu sun tare wata motar daukar gawa a babban titin Benin da ke jihar Edo sannan suka sace kanin da ke hanyarsa zuwa Enugu don yin jana'zar yayansa.

Duk da cewa ba su sace direban motar daukan gawar ba, harsashi ta kashe direban motar da ke bayan motar daukar gawar sakamakon bude wuta da yan bindigar suka yi.

'Yan bindiga sun tare motar ɗaukan gawa, sun yi awon gaba da ƙanin mamacin
'Yan bindiga sun tare motar ɗaukan gawa, sun yi awon gaba da ƙanin mamacin. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Abin da yasa jami'an tsaro ba za su iya gano yan bindigan da Gumi ya gana da su ba, Adamu Garba

Wani mazaunin garin Ahor a kan babban titin, mai suna Osamudiamen Odia ya shaidawa Premium Times cewa yana daya daga cikin wadanda suka ceto direban da ya fada cikin kwata bayan arangama da masu garkuwa.

Odia ya ce;

"Da ganin motar daukar gawar, yan bindigan sun bude wuta amma direban ya yi sa'a ya harsashin bai same shi ba. Amma harsashin ya samu direban motar da ke bayansa inda matukin motar ya mutu nan take.
"Harbin bindigan ya tilastawa direban ya yi tsayawar gagagwa kuma ya fada cikin kwalbati. Yan bindigan sun sace kanin mamacin da ke zaune a gaban mota sun shiga daji da shi.
"An dakatar da tafiyar saboda motar daukar gawar ta lalace. An kai gawar zuwa wani dakin ajiyar gawa a wata asibiti da ke Benin/Auchi a birnin Benin."

KU KARANTA: Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa

Yayin da an gano cewar masu garkuwar sun nemi a biya su Naira miliyan 5 kudin fansa, mai magana da yawun yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor ya ce an kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel