Abin da yasa jami'an tsaro ba za su iya gano yan bindigan da Gumi ya gana da su ba, Adamu Garba

Abin da yasa jami'an tsaro ba za su iya gano yan bindigan da Gumi ya gana da su ba, Adamu Garba

- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba, ya bayyana dalilin da yasa jami'an tsaro suka gaza gano yan bindiga

- A cewar Garba, Gumi ya ba makami ya dauka ba sai dai ya nemi su gana su tattauna ne domin ya saurari matsalolinsu ya shaidawa al'umma

- Adamu Garba ya bawa gwamnati shawarar ta duba yiwuwar tattaunawa da yan bindigan da nufin warware matsalolinsu a maimakon yaki

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba, ya ce akwai rashin gaskiya a yakin da jami'an tsaron Nigeria ke yi wurin dakile yan bindiga da yankin arewa maso yamma na kasar.

Ya ce fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi ya yi nasarar gano inda yan bindigan Zamfara suke ne har ya tattauna da su saboda ba yakarsu ya tafi yi ba.

Abin da yasa jami'an tsaro ba za su iya gano yan bindigan da Gumi ya gana da su ba, Adamu Garba
Abin da yasa jami'an tsaro ba za su iya gano yan bindigan da Gumi ya gana da su ba, Adamu Garba. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

Garba, a hirar da ya yi da The Punch a wani shiri na kai tsaye da aka yi a karshen mako ya ce yaki da aka yi bai samar da wani nasara ba tunda kasar ta fara yaki da yan bindigan tsawon shekaru 10 da suka shude.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa hotunan Sheikh Gumi da yan bindigan da aka dauka a Shinkafi da karamar hukumar Gummi ya karade shafukan sada zumunta a makon da ta gabata.

DUBA WANNAN: Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi

Sheikh Gumi ya ziyarci sansanonin yan bindiga a Zamfara domin yada sakon musulunci da zaman lafiya da nufin kawo karshen garkuwa da mutane da hare haren yan bindiga.

"Jami'an tsaro sun ce ba su san inda yan bindigan su ke ba amma hakan ba gasiya bane.

"Menene girman Nigeria? Don haka, za ku iya gano su amma matsalar shine za ku iya tunkarar su ku kawar da su ba bindiga? Wannan shine maganar. Jami'in tsaro zai tafi da Ak 47 dinsa da wasu bama-bamai da tankokin yaki, abinda ya ke son yin amfani da su kenan. Dole sai ya yi shiri amma iya saninsa, idan dai bai shirya tunkararsu ba, ba zai gansu ba.

"Amma shi Sheikh Gumi ya ce, 'Zaman lafiya na zo da shi, kuna iya caje ni, tattaunawa kawai na ke son muyi, menene matsalar ku don in sanar da al'umma matsalolin ku, hakan yasa suka ce, 'Shikenan, za mu yarda ka zo cikin aminci, za mu fada maka matsalolinmu sannan mu kyalle ka ta tafi cikin aminci.

KU KARANTA: Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze

"Idan da gwamnati za ta dauki irin wannan matakin, da abin ya fi sauki," wani sashi cikin abinda Adamu ya ce.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164