Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa
- Rundunar sojojin Nigeria sun yi nasarar damke wani, Adamu Umar, da ake zargi da garkuwa da mutane
- Kwamandan OPSH a Plateau, Chukwuemeka Okonkwo, ya ce an kama Umar ne bayan ya yi garkuwa da wata matar aure
- Okonkwo ya ce an kama Umar ne bayan an masa dabara an ce ya zo ya karbi kudin fansar ta N2m a wani wuri
Dakarun sojoji na Operation Safe Haven, OPSH, sun kama wani da ake zargin shugaban masu garkuwa ne, Adamu Umar, da ake zargin ya sace wata mata a jihar Plateau.
Kwamandan OPSH, Manjo Janar Chukwuemeka Okonkwo, wanda ya yi holen wadanda ake zargin a ranar Juma'a, ya ce Umar ya yi wa wata mata, Zuwaria Mohammed dabara ya kai ta Guratop a karamar hukuma Jos ta Arewa da sunan akwai kayan da zai sayar mata da su.
DUBA WANNAN: Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze
Bayan ta isa wurin sai ya tsare ta, ya tuntubi mijin ta, Rabiu Mohammed ya nemi a biya shi kudin fansa Naira miliyan 2 kafin ya sako ta.
Mijin matar ya yi korafi ga OPSH inda suka bashi shawarar ya amince zai biya kudin fansar.
"Mijin ya yi korafi zuwa ofishin OPSH inda suka bashi shawarar ya amince zai biya kudin fansa sannan aka amince da inda za a karbi kudin. Sojojin OPSH suka yi kwantar bauna a wurin da za a karbi kudin suka kama mai garkuwar suka ceto matar," in ji kwamandan.
KU KARANTA: Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi
Kwamandan ya kara da cewa an taba kama mai garkuwar sau biyu a baya kuma yana cikin jerin sunayen wadanda yan sanda ke nema ruwa a jallo saboda garkuwa.
A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.
Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng