'Yar Najeriya, Zainab Usman, ta ciri tuta a kasar Amurka, ta samu babban mukami

'Yar Najeriya, Zainab Usman, ta ciri tuta a kasar Amurka, ta samu babban mukami

- Yan Najeriya a fadin duniya na nuna bajintansu a bangarori daban-daban na rayuwa

- Wata mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Zainab Usman, ta samu mukami a Amurka

- Zainab Usman ta samu shiga Carnegie Endowment a matsayin diraktar harkokin Afrika

Wata 'yar Najeriya, Zainab Usman, ta ciri tuta a Amurka yayinda aka nada ta Diraktar harkokin Afrika a Carnegie Endowment.

An sanar da nadin Zainab ne ranar Talata, 2 ga Febrairu, 2021.

Zainab ta yi karatun doktoranta a jami'ar Oxford dake Ingila.

Tsokaci kan sabon mukamin da ta samu a Tuwita, Zainab ta ce wannan shiri na harkokin Afrika zai bada gudunmuwa wajen bada shawarin tattalin arziki, siyasa, fasaha, da abubuwan da suka shafi Afrika.

KU KARANTA: Ba zamu yarda wani ya taba yan kudu a Jigawa ba, Gwamna Badaru

Binciken da Legit.ng ta gudanar ya nuna cewa gabanin yanzu, Zainab ta yi aiki bankin duniya.

A bankin, tayi aiki kan cigaba tattalin arziki, tattalin ma'adinan kasa da kuma fasaha.

Ta yi aiki kan wadannan abubuwa a kasashe irinsu Cote d’Ivoire, Morocco, Nigeria, Papua New Guinea, the Republic of Congo, Serbia, Tanzania, da Uzbekistan.

'Yar Najeriya, Zainab Usman, ta ciri tuta a kasar Amurka, ta samu babban mukami
'Yar Najeriya, Zainab Usman, ta ciri tuta a kasar Amurka, ta samu babban mukami Credit: @ceu
Source: Twitter

KU KARANTA: Kasuwancin kiwon shanu ya fi na kudin intanet, in ji Adamu Garba

A wani labarun kuwa, Donald Trump ya cire tsohuwar asusun Gab din sa saboda dawowar da ya yi ta kafofin sada zumunta sakamakon gogewar da manyan kamfanonin fasaha na Silicon Valley suka yi.

A sakonsa na farko zuwa shafin tun ranar 8 ga Janairu, Trump ya daura martanin lauyansa kan bukatun da ya bayar da shaida a sauraren tsige shi karo na biyu mako mai zuwa.

Trump ya koma ga sakin bayanan ne daga Ofishin tsohon shugaban kasar bayan da Facebook, Twitter, Instagram, Reddit, Snapchat, Twitch, Shopify, Stripe, da YouTube, da sauransu suka datse.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel