Ba zamu yarda wani ya taba yan kudu a Jigawa ba, Gwamna Badaru

Ba zamu yarda wani ya taba yan kudu a Jigawa ba, Gwamna Badaru

- Gwamnan Jigawa ya yi tsokaci kan tsangwamar da ake yiwa Fulani a kudancin Najeriya

- Badaru yace yan kudun dake Arewa su kwantar da hankalinsu, babu wanda zai taba su

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya kwantar hankalin yan kudancin Najeriya mazauna jiharsa cewa shirye yake da karesu rayukansu da dukiyoyinsu.

Gwamnan ya bada wannan tabbaci ne ranar Asabar yayinda ya karbi bakuncin gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, a jihar Jigawa, Premium Times ta ruwaito.

Gwamna Badaru ya gayyaci takwaransa na Ebonyi ne domin kaddamar da wani hanya a karamar hukumar Babura.

Badaru ya yi amfani da daman domin jawabi ga Inyamuran da suka fita kwansu da kwarkwatansu domin tarban gwamnan na Ebonyi.

"Muna godiya mutan kudu na zaman lafiyansu a Jigawa tare da mu, kuma muna son bayyanawa kowa cewa ku kwantar da hankalinku a Jigawa da sauran jihohin Arewa," Badaru yace

"Ku fadawa yan siyasan dake son kawo rashin jituwa kasar nan cewa ba zasuyi nasara ba saboda babu wanda zai tayar da hankalin yan kudu a Arewa."

Gwamnan ya ce gwamnati ba zata zuba ido a cutar da wani a Jigawa ba.

A jawabinsa, Umahi ya godewa gwamnonin Arewa bisa kokarin samar da zaman lafiya a Najeriya.

DUBA NAN: 'Yar Najeriya, Zainab Usman, ta ciri tuta a kasar Amurka, ta samu babban mukami

Ba zamu yarda wani ya taba yan kudu a Jigawa ba, Gwamna Badaru
Ba zamu yarda wani ya taba yan kudu a Jigawa ba, Gwamna Badaru PHOTO CREDIT: @DavidNwezeUmahi2
Asali: Facebook

A bangare guda, tsohon dan takarar shugabancin Najeriya, Adamu Garba ya bayyana cewa saka hannun jari a kasuwancin kiwon shanu ya fi kowane nau'i na kasuwancin kudaden intanet da aka fi sani da cryptocurrency.

Adamu ya fadi hakan ne yayin da yake maida martani ga umarnin da Babban Bankin Najeriya ya baiwa bankuna na rufe asusun mutane ko kuma wadanda suke da hannu a cikin hada-hadar kudi a cikin tsarin su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel